Da yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaran aikinsa na kasar Venezuela Nicolás Maduro dake ziyarar aiki a kasar Sin a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
A yayin shawarwarin, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, Sin da Venezuela abokai ne na kwarai da suka amince da juna, kana abokan hadin gwiwa dake samun ci gaba tare.
Sin ta kiyaye raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Venezuela bisa hangen nesa a dogon lokaci, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Venezuela a kokarinta na tabbatar da ikon mulkin kasar, da martaba al’ummar kasar, da zaman lafiyar kasar, da nuna adawa da sauran bangarorin waje na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Venezuela. Sin tana son yin aiki tare da kasar Venezuela wajen tsara taswirar bunkasa dangantakar dake tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, ta yadda hakan zai amfanawa jama’ar kasashen biyu, da samar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya baki daya. (Zainab)