A jiya Asabar ne aka bude bikin yawon bude ido na birnin Shanghai karo na 34 a Shanghai dake gabashin kasar Sin, wanda zai gudana har zuwa ranar 6 ga watan Oktoba dake tafe, bikin da ke da nufin bunkasa hada hada a fannin yawon shakatawa.
Rahotanni na cewa, wuraren bude ido 70 dake birnin na Shanghai, za su bayar da rangwamen kaso 50 bisa dari ga masu ziyara, a tsakanin ranaikun 16 zuwa 22 ga watan Satumban nan. Kaza lika gundumomin birnin 16, za su kaddamar da ayyukan nishadantarwa daban daban masu nasaba da hakan.
A bana, bikin zai gudana ne a wasu kananan yankuna dake birane 12, na yankunan kogin Yangtze, da gabashin kasar Sin, ciki har da garin Suzhou na lardin Jiangsu, da Taizhou na lardin Zhejiang, da Huangshan na lardin Anhui, da Shangrao na lardin Jiangxi, da kuma Sanming na lardin Fujian.
Alkaluma daga hukumar gudanarwar birnin Shanghai, masu nasaba da harkokin raya al’adu da yawon shakatawa, sun nuna cewa, a watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2023, birnin Shanghai ya karbi masu ziyara na cikin gida sama da miliyan 139, ya kuma tara harajin yawon bude ido sama da yuan biliyan 155, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 21.59, adadin da ya karu da sama da kaso 100 a tsawon shekara guda. (Saminu alhassan)