Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) don yin wata ganawa kan yajin aikin da ta ke shirin yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Simon Lalong, ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya fitar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Roki NLC Da Ta Janye Shirin Tsunduma Yajin Aiki
- Yajin Aiki: Shugabannin NLC Sun Yi Watsi Da Gayyatar Da Gwamnati Ta Yi Musu
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Lalong a ranar 4 ga watan Satumba ya gayyaci NLC da kungiyar kwadago ta kasa (TUC) don yin wata ganawa da nufin dakile yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka fara yi a fadin kasar.
LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa TUC ce kadai ta halarci taron.
Lalong ya ce ya umurci ma’aikatar kula da ayyukan kungiyoyin kwadago da hulda da masana’antu da ta kira taron da shugabannin kungiyar ta NLC ranar Litinin.
Ya ce yana da kyau kungiyoyin kwadago su zauna da gwamnati domin warware duk wasu batutuwan da ke gabansu domin kaucewa ci gaba da kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.
“Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu za ta rika shiga cikin kungiyoyin kwadago da kuma amsa matsalolinsu bayan tuntubar juna da tattaunawa.
Lalong ya ce “Wannan don tabbatar da daidaiton masana’antu wanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban Ajandar Sabunta Fata.”
Haka kuma, a ranar 1 ga watan Satumba ne majalisar zartaswar kungiyar NLC ta kasa, a cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi barazanar shiga yajin aiki na tsawon kwanaki 21.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa NLC ta bukaci gwamnati ta kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa N200,000 da sauran bukatun da ta gabatar.