Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) za ta kafa Cibiyar Sadarwa ta Gaggawa a fadin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bada wannan tabbacin a wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai da aka gudanar a karshen mako a otal din Bristol Palace da ke Kano.
- Cire Tallafin Mai: Babu Shirin Karin Kudin Kiran Waya – NCC
- NCC Ta Bai Wa Kamfanonin Sadarwa Kwana 30 Don Warware Matsalolin Masu Amfani Da Layukansu
Danbatta ya ce kafa cibiyoyin ya zama wajibi domin dinke barakar da ke tsakanin hukumomin bayar da agajin gaggawa a kasar.
Danbatta ya kuma ce hukumar a karkashin jagorancinsa, ta kara yawan tallafin bincike da ake baiwa jami’o’in daga N20m zuwa N30m inda ya nuna cewa kawo yanzu jami’o’i uku ne suka ci gajiyar sabon tallafin.
“NCC a matsayinta na mai kula da harkokin sadarwa tana sane da cewa wayar sadarwa ce mai taimakawa da kuma samar da ci gaban tattalin arzikin kasa, kuma ta samar da sabis na sadarwa mai araha, mai da sauki don duba wasu shingen sadarwa,” in ji shi.
Shugaban na NCC ya ce, hukumar a matsayinta na hukumar da ke kula da ci gaban harkokin sadarwa, ita ce ta tabbatar da ingantattun ayyuka duba da yadda NCC na daya daga cikin sassan da suka taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce manyan kalubalen da ke gaban hukumar sun hada da lalata kayan aikin da gangan da kuma yawan harajin da ake dorawa kamfanonin sadarwa.
“Kalubalan da hukumar ke fuskanta sun hada da nau’ikan haraji 41 da aka dorawa kamfanonin sadarwa da lalata kayayyakin mu da gangan,” cewarsa.
A cewarsa, hukumar za ta ci gaba da hada kan masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai domin fadakar da jama’a game da ayyukan hukumar.