Wasu alkaluma daga kamfanin hakar ma’adanin karfe na Sin ko CNMC a takaice, sun nuna yadda yankin hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya na Zambia da Sin, ke kara samun ci gaba sannu a hankali cikin shekarun baya bayan nan.
Bayanan kamfanin na CNMC, wanda ya gina yankin sun nuna cewa, tun daga kafuwar sa a shekarar 2007, yankin hadin gwiwar raya tattalin arzikin ya jawo ‘yan kasuwa masu zuba jari kusan 100, wadanda suka zuba jarin da ya haura dalar Amurka biliyan 2.5.
A matsayin sa na yankin raya tattalin arziki mai sassa daban daban a kasar ta Zambia, yankin ya samar da guraben ayyukan yi sama da 10,000 ga al’ummun wurin da aka gina shi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)