Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce wakilai daga sama da kasashe 110, sun tabbatar da aniyar su ta halartar dandali na 3 na shawarar ziri daya da hanya daya, game da hadin gwiwar sassan kasa da kasa, wanda ke tafe a watan Oktoba mai zuwa.
Mao Ning, ta bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi mata tambaya game da shirin gudanar dandalin.
Ta ce dandalin zai kunshi bikin budewa, da manyan taruka 3 masu nasaba da hade sassa daban daban, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da raya tattalin arzikin zamani, kana za a gudanar da karin wasu dandalolin 6, masu nasaba da nazarin dabarun gudanar da cinikayya cikin sauki, da musaya tsakanin al’ummu, da musaya tsakanin masana da kuma sauran batutuwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp