Wani rahoto da aka fitar a Larabar nan ya nuna cewa a shekarar 2022, kasar Sin ce ta gabatar da kusan kaso 1 bisa 3, na jimillar takardun binciken ilimi da aka wallafa, a mujallun nazari na kasa da kasa mafiya daraja, wanda hakan ya sanya a karon farko kasar Sin din zarce Amurka, tare da zama ta farko a duniya baki daya a fannin.
Rahoton wanda cibiyar yada bayanan kimiyya da fasaha ta Sin, dake karkashin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar ko ISTIC ta fitar, ya nuna cewa, cikin takardun bincike 54,002 da aka wallafa a bara, a mujallu 159 mafiya kima, a muhimman fannoni 178, masu binciken Sin ne suka gabatar da takardun bincike 16,349. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp