Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da bullar cutar sarkewar numfashi wato (diphtheria) a jihar.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Dr. Salisu Mu’azu Babura, ne ya tabbatar da hakan.
- Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 520 — Gwamnatin Kano
- Cutar Mashako ‘Diphtheria’ Ta Kashe Dalibai 2, Gwamnati Ta Kulle Makarantu A Bauchi
Muazu ya tabbatar da cewa kimanin mutane 91 da ake zargin sun kamu da cutar.
Kazalika ma’aikatar lafiya ta jihar tace a kwai rahoton yara goma da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.
Dakta Salisu Mu’azu, ya ce sun gano wasu mutane biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun. Salisu ya ce yanzu haka an tura karin samfurin jinin wadanda ake zargin sun kamu da cutar zuwa Abuja domin yin gwaji.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar Jigawa ta himmatu wajen ganin an shawo kan lamarin.
Daga: Abdullahi Yawale