Daga jiya Juma’a zuwa yau Asabar, an gudanar da taron kasa da kasa na kula da harkokin masana’antu da kasuwanci bisa doka a birnin Beijing, fadar mulki kasar Sin. Inda kungiyar inganta aikin ciniki ta kasar Sin ta gabatar da sanarwar Beijing, a madadin manyan kusoshi masu sana’o’in masana’antu, da kasuwanci, da doka, da suka halarci taron.
Sanarwar da aka gabatar ta kunshi bayanai masu alaka da kare tsarin ciniki, wanda ya shafi bangarori daban daban, da tabbatar da amfanin dokoki ta fuskar kare moriyar kamfanoni, da zurfafa cudanyar da ake yi a fannin kulawa da harkoki bisa doka, da karfafa hadin kan sassa daban daban, don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duk duniya, da dai makamantansu. (Bello Wang)