An yi kira ga malaman addinin musulunci da cewa kada gudunmawar da suke samu daga ‘yan siyasa ta rude su.
Farfesa Azeez Taofiq ne ya yi wannan kiran a wajen wani taro na yini daya da aka shirya ga malaman addini a Sakkwato. Kamar yadda Daily trust ta ruwaito.
Gidauniyar Alhabibiyya tare da tallafin gidauniyar MacArthur ce ta shirya taron.
A cewar Farfesa Taofeeq, cin hanci da rashawa ne ke haifar da duk wani sharri, ya kara da cewa rashin tsaro da ya addabi kasar nan (Nijeriya) ya samo asali ne sakamakon cin hanci da rashawa.
“Mun zo nan ne domin mu gaya wa malamanmu da su yi amfani da harsunansu, su yi kira ga Jama’a akan daina fasadi.
“Kada gudunmawar da ‘yan siyasa ke basu ta shagalantar da su wajen fadan gaskiya.” Inji Farfesa Taofiq.
Shima da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar Alhabibiyya na kasa, Ustaz Adeyemi Fu’ad, ya bayyana cewa, an shirya wannan taron ne domin wayar da kan mahalarta taron kan bukatar dogaro da kai da kuma yaki da cin hanci da rashawa.