Karamin ministan tsare tsaren tattalin arziki na kasar Angola Jose de Lima Massano, ya jinjinawa tasirin jarin Sinawa ‘yan kasuwa a Angola, wanda a cewar ministan ya taimaka matuka wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar.
Mista Massano, ya bayyana hakan ne yayin taron kungiyar raya cinikayya ta Angola da Sin ko CAC, da kamfanoni mambobin kungiyar, wanda ya gudana ranar Asabar a birnin Luanda, fadar mulkin Angola. Ya ce kamfanonin ‘yan kasuwa Sinawa masu zaman kan su, sun zuba jari a Angola wanda hakan ya haifar da damammakin samun kudin shiga ga ‘yan kasar.
- Kasar Sin Ta Aike Da Kayayyakin Agajin Gaggawa Zuwa Kasar Libya Da Ambaliyar Ruwa Ta Afkawa
- Han Zheng Ya Yi Kira Ga Sin Da Amurka Da Su Kyautata Matakan Shawo Kan Sabani
Kaza lika, mista Massano ya ce dalilin gudanar da taron shi ne bunkasa tattaunawa tsakanin kamfanonin Sin da na Angola, da sashen raya tattalin arziki na gwamnatin kasar.
A nasa tsokaci, shugaban CAC Luis Cupenala, wanda ke wakiltar kamfanonin Sinawa masu zaman kan su a taron, ya gabatar da bayanai da shawarwari, ciki har da batun yarjejeniyoyin kare jarin da aka zuba, da kyautata tsarin fitar da hajoji, da inganta yanayin gudanar da kasuwanci.
Game da hakan, mista Massano ya ce gwamnatin Angola, za ta ci gaba da warware wadannan batutuwa, da taimakawa kamfanoni wajen kawar da kalubalen da ake fuskanta, da kara inganta yanayin gudanar da kasuwanci ga kamfanonin ketare masu zaman kan su, ta yadda hakan zai bunkasa dunkulewar sassan ci gaban Angola. (Mai fassara: Saminu Alhassan)