Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan bindiga a jihar Zamfara a asirce ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.
Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani a wata takarda da ya aike wa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara wanda ya yi zargin cewa, gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan ta’addan Zamfara domin ganin an sako mutanen da aka sace.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Gwamna Lawal Ya Mai Da Martani Ga Ministan Labarai
- Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
Ministan ya yi watsi da zargin, yana mai nuni da cewa “Gwamnatin Tarayya tana aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto ‘yan matan jami’an tarayya ta Gusau da sauran wadanda aka sace sun sake hade wa da iyalansu.
Ministan, a cikin wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro (MOD), Attari Hope, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana kwarin guiwar cewa, jami’an tsaro na hadin guiwa da ke aiki ba dare ba rana za su ceto daliban.
Ministan ya ce, “zargin karya ne kuma yaudara ce domin ma’aikatar tsaro ba ta umurci wani ko wata kungiya da su tattauna a madadin gwamnatin tarayya ba.”