Yayin da ake cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da tunanin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, a jiya ne Sin ta gabatar da takardar bayanin mai taken Hada kai wajen karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama: Shawara da matakan Sin, wanda ya bayyana shirin kasar Sin na bukatar jama’ar kasa da kasa da su hada kai wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya da samun wadata tare.
Kasar Sin ta gabatar da shawarar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, tare da daukar alhakin aiwatar da shawarar yadda ya kamata. Takardar ta yi bayani game da kira da ayyukan da Sin ta gudanar game da sa kaimi ga gina al’ummar duniya mai makomar bai daya a fannoni hudu, wato sa kaimi ga raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aiwatar da manyan shawarwari guda uku a duniya, da shiga aikin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya, da kara kuzari ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a dukkan fannoni. (Zainab)