Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar Mauludin Annabi (S.A.W) na shekarar 2023.
Jami’in hulda da jama’a na ofishin shugaban ma’aikatan jihar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a fadin jihar a ranar Laraba.
- Bukukuwan Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta.
- Cutar Mashako Ta Kashe Yara 14 A Jihar Jigawa
Shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad Dagaceri, ya ce, gwamnan jihar, Alh. Umar Namadi ya amince da yin hutun na Mauludi a gobe Alhamis.
“Ina mai sanar da cewa gwamnati ta ayyana 12 ga R/Awwal, 1445AH (28 ga Satumba, 2023) a matsayin ranar hutu don murnar Mauludin Annabi Muhammad (S.A.W),” cewar sanarwar.
Sanarwar ta umarci ma’aikata da daukacin al’umar musulmin jihar da su yawaita yin addu’o’in samun zaman lafiya yayin gudanar da Mauludin.