Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce, sama da masu son yin aure 4,000 ne suka yi rijista a cikin shirin aurar da mutane da gwamnatin jihar Kano ta shirya yi a wata mai zuwa.
Hukumar ta kara da cewa ta samu nasarar tantance ma’aurata 1,800 kuma tuni aka shirya musu gwaje-gwajen lafiya a wani mataki na cike sharadin yin auren ga mutanen.
- Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Naira Miliyan 600 Wajen Gudanar Da Ayyuka A Kasuwar Hatsi Ta Dawanau
- Magidanta 137,000 Sun Ci Gajiyar Rabon Kayan Abinci A Kananan Hukumomi 6 Na Jihar Yobe
Mataimkin kwamandan Hisba a sashin ayyuka, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya ce, ma’auratan da aka zaba za a musu gwaje-gwajen cutar nan mai karya garkuwar jiki da gwajin kwayar halitta da kwajin shaye-shaye kafin a sanya su cikin jerin mutane na karshe da za a dauki nauyin aurar da su a wata mai zuwa.
Mujahid ya ce a karin farko gwamnatin jihar na da niyyar aurar da mutum 1,800, amma zuwa yanzu masu son kasancewa ma’aurata sama da 4,000 ne suka zo hukumar suka yi rijista.
Malam Mujahid ya kara da cewa sakamakon matsatsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan, mutane da dama su na son shiga tsarin auren gama-gari musamman ‘yan mata da mata da iyayensu ke son aurar da su tun da jimawa amma sakamakon tsadar aure ba su iya samun damar yin auren ba.
Ya shawarci wadanda za su ci gajiyar shirin da su kasance masu rayuwa cikin kwanciyar hankali da hakuri da juna.