Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da ke jihar Bauchi a ranar Alhamis ta kori karar da Arch. Khalid Abdulmalik Ningi na jam’iyyar APC ya shigar da ke kalubalantar ayyana Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya da INEC ta yi, bisa cewa korafin bai da inganci.
Don haka ne kotun ta tabbatar da nasarar da PDP da dan takararta Y. Suleiman suka samu. Shi dai Abubakar shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi a halin yanzu.
- Kungiya Ta Nemi ‘Yan Adawa Su Rungumi Kaddara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Bauchi
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar da Matsalar Tsaro
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa dangane da hukuncin, Y. Suleiman, ya yaba wa kotun bisa hukuncinta da ta yi amfani da hujjoji da tsarin shari’a wajen tabbatar da adalci ba tare da jin tsoro ko goyon bayan wani ba.
Ya ce, wannan kyakkyawar hukuncin zai kara bunkasa harkokin dimokuradiyya ba kawai a jihar Bauchi ba har ma da kasar baki daya.
Abubakar ya gode wa Allah bisa wannan nasarar da ya sake ba shi.
Har-ila-yau, Kakakin ya gode wa al’ummar mazabar Ningi ta tsakiya a bisa amincewa da suka yi suka sake zabinsa domin ya wakilce su a karo na biyu, ya sha alwashin cewa zai ci gaba da zage damtse wajen nema musu ababen more rayuwa da wanzar musu da ribar dimokuradiyya.