Mai daukar wutar yola na digital, bas marasa matuki da aka yi ta fasahar AR, dandalin ba da hidima kan kallon wasanni na zamani……Wasannin Asiya karo na 19 da har yanzu ake gudanarwa a birnin Hangzhou na kasar Sin na cike da alamun fasaha ta zamani, wanda ya haifar da zazzafar tattaunawa a tsakanin kasashen duniya.
Wasannin Asiya na Hangzhou shi ne wasannin Asiya na farko a tarihi da ya gabatar da manufar shirya wasanni ta fasahar zamani. An san Hangzhou da sunan “Birnin Dijital” na kasar Sin, lardin Zhejiang da birnin ke ciki, ya kasance a sahun gaba wajen zamanantar da kasar Sin, kuma yana kokarin samar da sabbin alfanu ga ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire. Don haka, ana iya cewa, “Wasannin Asiya na zamani” wata taga ce mai kyau wajen duba yadda ake zamanantar da kasar Sin.
- Xi Ya Jaddada Kara Kaimi Wajen Shiga Cikin Garambawul Na WTO Da Karafafa Ikon Bude Kofa Ga Waje
- Yadda Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Jagoranci Aikin Raya Lardin Zhejiang
Yin kirkire-kirkire hanya ce ta farko da ake bi wajen inganta zamanantar da kasar Sin, kuma “Wasannin Asiya na zamani” wani sashe ne dake iya bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yin kirkire-kirkire a cikin ‘yan shekarun nan.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, yawan kudin da kasar Sin ta zuba kan nazari da habaka ya karu daga kashi 2.1% zuwa sama da kashi 2.5%, kuma yawan gudummawar da aka bayar a fannin ci gaban kimiyya da fasaha ya karu zuwa sama da kashi 60%. Ana ta samun sabbin nasarori a wasu fannonin da suka shafi aikin kumbon da ke daukar ‘yan sama jannati, manyan na’urori masu kwakwalwa, da bayanan adadi da dai makamatansu.
Rahoton alkaluman yin kikire-kirkire na duniya na shekarar 2023 da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya ta fitar a jiya Laraba 27 ga wata, ya nuna cewa, kasar Sin ta zo matsayi na 12 a shekarar da muke ciki, kuma ita ce kasa daya tilo mai matsakaicin karfin tattalin arziki a cikin kasashe 30 dake kan gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)