Yau ranar bikin tsakiyar yanayin kaka na gargajiya na kasar Sin. Bikin ya samo asali ne daga bautar gunkin wata, ana amfani da “cikakken wata” don alamta “haduwar iyali”. A dubban shekarun da suka wuce, bikin wannan rana na dauke da kyawawan fatan jama’a na neman haduwa da juna, kuma yana kunshe da kaunar da jama’a ke nunawa gida da kasarsu.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi magana game da garinsa. Shaanxi shi ne garin Xi Jinping, inda ya yi aiki kuma ya rayu tsawon shekaru. A karshen shekarun 1960, Xi Jinping ya yi aiki a matsayin manomi a wani karamin kauye da ake kira Liangjiahe da ke garin Yan’an na lardin Shaanxi, kuma ya shafe shekaru bakwai a can. A watan Oktoba na shekarar 1975, kafin ya bar Liangjiahe, Xi Jinping ya fadawa wa ‘yan uwa mazauna kauyen cewa, “Zan bar wannan wuri, in koma birni don yin karatu a jami’a. Ba zan taba mantawa da duk abin da Liangjiahe ya ba ni ba.”
- Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a
- Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar
Bayan shekaru fiye da talatin, a shekarar 2013, Xi Jinping, wanda ya riga ya zama shugaban kasar Sin, ya ziyarci kasar Costa Rica, a lokacin da ya ziyarci wani gidan manomi, ya bayyana yadda yake aikin noma a Liangjiahe. “Shugabannin kasa kadan ne ke alfahari da kasancewarsu manoma a da”, in ji dan wani manomi, “Mai yiwuwa wasu shugabanni ba za su iya ambatar wannan kwarewa ba, amma Xi Jinping ba haka yake ba.
Daga kauyen Liangjiahe zuwa gundumar Zhengding, daga lardin Fujian zuwa lardin Zhejiang, birnin Shanghai, da na Beijing, sa’an nan kuma har zuwa zabensa a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS, shugaban kasa, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya, Xi Jinping ya kan kai sahihiyar kauna ga mutane a duk inda ya tafi.
A lokacin da yake gudanar da mulkin babbar kasa mai yawan al’umma sama da biliyan 1.4, Xi Jinping, ya mayar da kaunar da yake nunawa gari, dangi da kasarsa zuwa ga ci gaba da sadaukar da kai don tabbatar da samun ingantacciyar rayuwa ga daukacin Sinawa, har ma ya ce, “Zan zama mara son kai kuma ba zan ci amanar mutane ba.” (Mai fassara: Bilkisu)