Sakatare Janar na tawagar kasar Sin a gasar wasannin Asiya dake gudana a Hangzhou ya bayyana a yau Asabar cewa, tawagar kasar Sin ta shiga gasar da kafar dama tare da karafafa matsayinta na jagora a yawan lambobin yabo, kuma ta zarce yadda ake tsammani.
Zhang Xin ya bayyana hakan ne yayin da gasar wasannin Asiya ta Hangzhou ta kai rabi.
Zhang ya ce, “‘yan wasan kasar Sin sun fafata cike da karfin gwiwa, inda suka taka rawar gani a fagen wasa, kuma suna ci gaba da samun sakamako mai kyau,” Zhang ya kara da cewa kasar Sin ta lashe lambobin zinare 107 ya zuwa yammacin ranar Asabar. “Kasar Sin ta fara gasar da kyau, kuma ta ci gaba da samun nasarar lashe lambobin zinare, inda ta kasance kan gaba wajen samun lambobin zinare da babban rata.” (Yahaya)