Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na Ado Da Kwalliya.
Uwargida a matsayinki na wadda take so ki zauna lafiya sannan ki mallaki mijinki ta hanya mafi sauki, kuma sannan kina tsarki da ruwan sanyi, duk sanda kika ji fitsari ruwan sanyi ne abin yin tsarkinki, to tabbas wannan hanya ce da kike kashe kanki da kanki da hannunki, domin shi ruwan sanyi yana wargaza mace.
Yin tsarki ga ‘ya mace da ruwan sanyi yana haifar mata da faruwar cututtuka da dama, daga cikin su akwai : Cutar ciwun sanyi wato (Infection), wanda a yanzu shi yake addabar mafi yawancin mata, sannan akwai kaikayin gaba, akwai kurajen gaba, da warin gaba da dai sauran su.
Saboda haka Uwargida da kike so ki zauna a gidanki lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali ke da maigida ina baki shawara da ki de na yin tsarki da ruwan sanyi.
Idan kina tsarki da ruwan sanyi to ga dama ta samu saboda ki magance wadannan cututtuka idan kin kamu da su, ko da baki kamu da su ba za ki iya hadawa saboda yana gyara mace sosai, yana matse mace, ya saukar mata da ni’ima, sannan yana sa jin dadin mu’amala tsakaninki da maigida.
Abubuwa da za ki samu:
Bagaruwa tamu ta gida ta Hausa, ganyen magarya, lalle, kanun gari amma kadan.
Yadda za ki hada su:
Za ki samu tukunyarki mai kyau sai ki kawo wadannan abubuwa da muka ambata ki zuba amma ki dan dauraye su sai ki zuba ruwa daidai yadda kika ga ya isa sai ki dora a wuta ki bar shi ya dan tafasa sosai, za ki iya zuba dan gishiri kadan a ciki shima yana da amfani sosai sai ki dinga tsarki da wannan ruwan za ki ga yadda za ki ji dadin jikin ki da kuma mu’amalar aure.