Shafin da ke zakulo muku batutuwan da suka shafi al’umma na Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Aure, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu samarin ke kashe kudadansu wajen ‘yan mata ba tare da sun taimaka wa iyayensu ba, ko da kuwa iyayen ba su da kudin kashewa. Wannan al’amarin ya zama tamkar abun ya yi a yanzu wajen matasa, duba da yadda wasu ke iya kashe kudinsu wajen siyen tufafi dan bawa budurwa a sabgogin da ba su zama tilas wajenta ba, irin kashe kudin da ya zama tamkar almubazzaranci a wajenta, wanda kuma saurayin ne ke daukar dawainiyar hakan. Ya yin da aka yi duba ga mahaifansa sai ka ji tamkar ka zubar musu da kwalla sabida tsabar tausayin rasa kudin amfanin cikin gida, wanda kuma dansu na da shi amma baya yi, wani ma ko sana’ar arziki ba shi da ita a haka zai tare wajen budurwa ba tare da ya taimakawa kansa ko iyayensa ba. Wannan dalilin ya sa muka ji ta bakin mabiya shafin Taskira game da wannan batu; Ko mene ne amfanin kashe wa ‘yan mata kudade ba tare da an tallafawa iyaye ba?, Ta wacce hanya za a ganar da masu irin wannan dabi’a?. Ga kuma bayanan na su kamar haka:
Sunana Sadiya Garba Umar Jihar Kano:
Ai wadannan mutane su ake kira da samarin shaho Hajiya, kawai su burgewar su su yi wanka su saka kaya masu kyau su saka ‘yan canji a aljihu koda cikinsu babu komai a cikinsa, wannan sam! bai da amfani, domin duk aikin da za ka yi shi babu lada wallahi aikin banza ne, daka dauki naira goma ka bai wa wata can a waje wadda ka san ba ma aurenta za ka yi ba, gwara ka dauki naira biyar ka bai wa mahaifanka ko ba komai Allah zai baka lada. To ganar da irin wadannan mutanen gaskiya ba abu ne me sauki ba, saboda kana fara gaya musu ma cewa za su yi kai ba ka waye ba, ba ka san dadin rayuwa ba, amma idan har Allah ya hada ka da mai rabon shiriya sai ka nuna masa cewar ba abin da ya fi iyaye muhimmanci a rayuwa, komai ka samu kafin ka fara tuna kowa ka fara tunawa da iyaye, domin sune jigonka kuma tsani na rayuwar ka. To musamman iyaye ku sani itace fa tun yana danye ake fara tankwara shi domin idan ya bushe wallahi ba zai taba lankwasuwa ba, in ka matsa masa ma yana iya karyewa wa’iyazu billah. Yawanci iyaye suna sakaci wajen tarbiyyar yara, musamman yaranmu maza da suke ganin da sun fara girma shike nan sun fi karfin a sa su, su yi abu sai su dinga ganin ma sun fi ki sanin abin da ya dace.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya duk saurayin da yake da wannan hali to zai yi wuya ya samu abin da yake so ko yake nema, domin taimakawa iyaye wajibi ne muddun mutum yana da rai da lafiyar da zai nema, domin taimaka musu zai sa su ji dadi suna yi wa mutum addu’ar da za ta sa ya samu nasara a neman auren da ya yake. To shi ihsani yana da dadi kuma abu ne mai kyau a lokacin neman auren, amma ba wai ka dauki dawainiyar mace gabaki daya ba, kuma yana da kyau ka na yin ihsanin da kyakkyawar niyya domin ko ba a baka aurenta ba ka samu ladan kyautatawa. To da farko idan mutum mai fahimta ne sai a yi masa nasiha da kyakkyawan lafazi da kuma hikima a nuna masa muhimmancin iyaye da kuma wajibcin kyautata musu domin neman kyakkyawan gobe. To akwai bukatar ‘yan mata su sani duk saurayin da yake da irin wannan hali to ke matar sa idan ya aure ki zai iya watsi da ke, domin iyayensa su ne silar zuwansa duniya amma ya yi watsi da su, don haka ke ma watarana zai yi watsi da ke. Iyaye kuma ya kamata su ci gaba da yi wa ‘ya’yansu masu irin wannan hali addu’ar shiriya. Su kuma samari ya kamata su yi karatun ta nutsu wajen neman aure, domin kaucewa neman auren matar da za ta raba ka da iyayenka ko ma ace aljannar ka, daga nan nake addu’ar Allah ya sa mu dace duniya da lahira.
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse Jihar Kano:
Hakan bai kamata ba domin iyaye suna gaba da komai, ba shi da wani amfani domin albarkar iyaye tana tare da mutum a dukkan al’amuransa. Ta hanyar yi musu wa’azi da nasihohi da kalmomi masu dadi. Iyaye su kula da ‘ya’yansu su san me suke aikatawa a waje, su kuma iyayen ‘yan mata su gane wannan hidimar ta samari ba ita ce abun dubawa ba, rayuwar da za a yi bayan Aure ita ce me muhimmanci.
Sunana Balkisu Musa Galadanchi Jihar Sokoto:
Wakika wannan abu ne da yake faruwa a wannan al’ummar ta mu, ya kasance gaba daya samarin wannan zamanin sun fi bai wa ‘yan mata muhimmanci sama da iyayensu, ina fatan malamai su rika yin wa’azi wa samari akan wannan abin. Babu ma amfani a ciki, indai har za ka dubi ‘yan mata ka yi musu abu ka manta iyayenka to bana ji akwai amfani muddin ba kana taimakawa iyayenka ba ne. Wa’azi, malamai su fara ankarar da su, gidajen rediyo da talabijin da jaridu su fara shirya shiri mai taken ankarar da samarinmu, wannan zai taimaka sosai. Shawara ita ce; iyaye su farka tun yaransu suna tasawa su rika taimakonsu da shawarwari saboda gaba.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya wannan halin na samari ba sa kyautawa, kuma ba daidai bane, don cutar da kai ne. Sannan rashin sanin ciwon kai ne, asara ce ma a takaice, dainawa ya fi dai. Kashewa ‘yan mata kudi ba tare da tallafawa iyaye ba ba shida wani amfani, kuma mutum ba zai ga albarkar abin ba, don kaucewa hanya ne ma gaba daya, iyaye su ne mafi cancanta da kowacce irin kyautatawa. Ta hanyar zama da su a yi musu nasiha, da fadakarwa da jan hankali. Da kuma nuna musu muhimmancin yi wa iyaye kyautatawa da yi musu hidima ba ‘yan mata ba, sannan a yi musu nuni da wasu da hakan ya faru a kansu don ya zama izna. Hanyoyin gyara ga iyaye, ‘yan mata da smarin sun hada da yi wa iyaye bayani akan abin da dansu yake yi don ja masa kunne, da kuma yi masu fada da nasiha akan barin wannan halin don samun ci gaban rayuwa. Sannan su ma ‘yan mata a yi musu bayani akan abin da samarin suke yi ba halin kwarai bane, don ko ma an yi auren ba za a samu zaman lafiya ba da kwanciyar hankali ba don babu albarkar iyaye, don haka su rinka yi musu nasiha da yi wa iyaye hidima ba su ‘yan matan kawai ba. Sannan samarin a yi musu duk nasiha da janhankali akan abin da suke yi, don ganin ci gaban haduwarsu da yin aurenma gaba daya.
Sunana Ibraheem Isma’el Jihar Kano Gezwa Jogana:
Bai kamata ba, ya zama inuwar giginya na nesa ka sha san yi, duk mutumin da yake so ya gama da duniya lafiya kana so ka ga daidai a rayuwa, Uwa Uba ko ba su tambaye ka ba ya kamata ace indai Allah ya hore ma ka ba sai sun tambayeka ba, ya kamata ka kyautata musu, ba a ce kar ka kayutatawa macen da ka ke so ba, amma komai za ka yi ka fara yi wa gida kafin ka kai nesa. Domin gida ko ya ya ka kyautata musu albarka ce za ta yi ta binka duniya da lahira, komai kasa a gaba indai kana yi musu Allah zai dinga dafa maka, bai da amfani ka dinga kashewa mace kudi dan faranta mata, wata duk lokacin da ba kada shi kai da banza duk daya tunda me bi dama dan abin hannun naka ake sonka, amma ba yadda za a kyautatawa gida dan ka rasa a dinga yi maka kallon banza ko a dinga ce maka dan wahala ba za a fada maka ba, Allah ya bada ikon gyarawa. Shawara da zan bawa mata da maza shi ne; mace kar ta yaudari kanta ta dinga jin dadi namiji yana kashe mata kudi shi ma ta iya yuwa akwai abin da yake nema daga ya samu shikkenan kin zama banza ba za ki kara ganinsa ba, kuma maza mu ji tsoran Allah komai kai za a yi maka, iyayenmu kuna kokari ku kara kokari wurin bibiyar yarinya ina take samun kudi?, da raba ‘ya’yanku da abokanan banza don duk tarbiyyar da ka bawa ‘ya’yanka indai akwai abokanan banza sai sun lalata maka, Allah ya sa a gyara.
Sunana Lawan Isma’il (Abu Amfusamu) Jihar Kano, Rano:
Maganar gaskiya ana samun ire-iren wadannan mazajen ba ma a maza ba, ana samun mata wadanda suke dan kulle-kullen su suna bawa saurayin nasu bayan sun san a gida ana da bukata din. Amma an fi samu a cikin maza kuma gaskiya abin da zan iya cewa akan wannan kamata yayi ka yi wa yarinyar da kake nema da aure kuma da gaske iya abin da ka ke da damar yi wa mace ka yi iyaka karfinka, amma ma fi kyau shi ne ka fara taimakawa gidanku sannan kai kanka ta inda koda tseguminka aka kaiwa yarinyar ko wani nata akanka za ka fita kunya sabida idan ka dauki waccan hanyar ba mai dorewa ba ce duba da zaman aure bana karya bane yau da gobe ta ki wasa. Amfaninsa iya kai da budurwar ne, hanya daya ce kawai su sani ita soyayya tana iya canjawa amma iyaye ko ba za ka taba canja su ba, shawarata anan ita ce duk abin da za a yi, a yi iya karfi. Sannan ke da ake yi wa wannan abin ki sani a yanzu wasu samarin ba don Allah da kuma son gaske suke kashe miki wannan kudin ba, kin san me nake nufi. Samarin ku ji tsoron Allah ku taimakawa iyayenku, kuma iyayen ita yarinyar akan kana yi mata abin da ya wuce kima bance kada kayiwa wadda kakeso hidimaba amma kayi mata wanda koda zaman aure ku ka zo za ta san cewa baka yi mata karya ba a rayuwarka. Su kuma iyayenmu kamata ya yi suna saka idanu ga yayansu, musamman iyayen ‘yan matan ko don a tsira da mutunci a idon saurayin da ma duniya baki daya.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi (Dr. Haibat) Jihar Kano:
A wannan lokacin samari da yawa suna mantawa da dumbin ladan da ake samu irin na dan da ya faran tawa uwar sa, wannan yana daya daga rashin karatu saboda da ilimin dole zai yi kokarin farantawa mahaifi, ita buduwar a ko wani lokacin za ka iya rabuwa da ita, ita kuma mahaifiya ta fi karfin wasa, saboda ita ce rayuwar ka, Ya kamata samari su san abin da ya kamata dan Allah a rinka kokarin faran tawa iyayye ko dan goben yaranmu, shi so ba sai da kudi ake yi ba, farin ciki, nishadi, nutsuwa, tausayi da iya magana shi ake kira da so ita kuma mace a koda yaushe burinta saurayi ya bata, ya kamata ki san cewa shi ma fa yana da nashi bukatun, ga na iyaye da kanne ba komai ake tambayar saurayi ba.
Sunana Zulkifilu Lawal {Naka Sai Naka}:
Aikata hakan ba hanyar neman albarka bace ba in har kana son ganin albarka a hidimarka ka fara kyautatawa iyayenka sannan wani ya biyo bayansu, rashin amfanin hidimtawa budurwarka kafin iyayenka shi ne duk hidimar da za ka yi wa budurwarka babu sanya albarka ko kuma neman lada a cikinta kana aikata hakanne domin ka samu soyayyarta da zarar kun samu matsala a tsakaninku shikenan kayi aikin banza, a karshe kuma ka yi da-na-sani masu aikata hakan su sani cewa ribar da ke cikin hidimtawa iyaye da kuma sanya albarkar su a dukkan al’amuranka ba abun wasa bane, ya kamata ‘yan mata su sani yawan karbar hidimtawa daga wurin saurayi yana rage wa mace kima a wajensa, wasu lokutan ma yana yi mata kallon makwadaiciya, sannan kuma zai iyayin amfani da wannan damar ya bata maki rayuwa ya kamata samari su fara hidimtawa iyayensu kafin ‘yan matansu, domin neman albarkar su a dukkan al’amuranka. Sannan iyaye su rinka kulawa da yadda ‘ya’yansu suke gudanar da rayuwarsu tare da tsawatarwa a dukkan kuskure idan sun aikata shi, domin kaucewa aikin da-na-sani Allah ya sa mu dace amin.