Jagoran Alkalan Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Nasarawa, Justice Ezikel Ajayi, ya bayyana cewa, bayanan da na’urar zabe ta BVAS da IREV suka bayar ya bambamta da Wanda aka rubuta a takarda.
Alkalin ya soke zunzurutun kuri’un da aka bewa dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC wadanda ba suyi dai-dai da na BVAS ba.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Tsige Gwamnan Nasarawa Na APC Ta Ayyana Umbugadu Na PDP
- ‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar
Sabida haka ne, mai shari’ar ya kwace sakamakon da ya ayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar gwamnan ta mayar wa Jam’iyyar PDP.
Alkalan Kotun guda biyu sun dogarane da wannan hujar inda sukace Gwamna Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC bai kai ga nasara ba. Don haka kotu ta tabbatar da nasarar mai kara Hon. David Emmanuel Ombugadu na Jam’iyyar PDP a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Nasarawa.
Da yake zantawa da manema Labarai a gidan Gwamnati jim kadan bayan zartar da hukuncin kotun, Gwamna Abdullahi Sule ya ce, “Duk da hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke, har yanzun ni ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Kuma zan daukaka kara zuwa kotun gaba.
“Ina kira agareku magoya bayana da kuyi hakuri da abinda kuka ji. Ina nan a matsayin Gwamna, zamu daukaka kara. Wannan hukunci ne na kotun sauraron kararrakin zabe ba na Kotun koli ba.
“Kuma zan ci gaba da yin ayyukan ci gaban kasa kamar yadda muke yi. Duk abinda za a fada muku, kar ya bakanta muku rai. Allah yakan jarrabi Bawa ta yadda yaso.”