Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da shirin raba buhunan shinkafa 43,000 mai nauyin kilo 50 domin rage radadin cire tallafin fetur da gwamnatin tarayya ta yi a baya.
Gwamna Uba Sani ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai jim kadan bayan duba kayayyakin da za a raba a wani dakin ajiyar kaya da ke Kaduna.
- Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Sabbin Shirye-shiryen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 Tare Da Cafke 9 A Jihar Kaduna.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, gidaje 210,000 na masu karamin karfi za su ci gajiyar shirin rabon tallafin a kashin farko na rabon tallafin a jihar.
Gwamnan ya yabawa kwamitin kula da jin dadin jama’a karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, bisa yadda suka gudanar da aikin cikin himma da kwazo.
Ya ce, an tanadi isassun tsare-tsare domin tabbatar da cewa, kayayyakin tallafin sun isa zuwa wurin rabon kayayyakin abincin ba tare da wata tangarda ba da kuma jigilar kayayyakin zuwa kananan hukumomi daban-daban da ke jihar.
Gwamnan ya ce, an kuma kafa wata tawagar masu sanya ido ta musamman da suka hada da kungiyar kwadago, kungiyoyin addini, cibiyoyin sarakunan gargajiya, kungiyoyin masu bukata ta musamman (nakasassu), ‘yan majalisar jiha, shugabannin kananan hukumomi, da wakilan gwamnatin jihar da kuma Kwamitin rarraba kayayyakin abincin.