Asibitin Dawanau da ke Kano, asibiti ne da gwamnatin Jihar Kano ta kirkire shi domin duba marasa lafiya da suke fama da matsalar kwakwalwa.
Amma a watan Yuni na wannan shekarar gwamnatin Jihar Kano ta damka asibitin a hannun gwamnatin tarayya don ci gaba da kula da shi.
- An Gurfanar Da Mutane 14 Kan Karyar Bacewar Mazakuta A Abuja
- Jami’ar Danfodiyo Ta Musanta Harin ‘Yan Bindiga A Harabar Jami’ar
Dokta Auwal Salihu, wanda ke shugabantar asibitin ya bayyana cewa a wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar, ya nuna duk cikin mutum dari akwai biyar da ke fama da matsalar kwakwalwa.
“Don haka akwai kusan mutum miliyan daya a jihar Kano da suke fama da matsalar kwakwalwa, sun sani ko kuma ba su sani ba, amma suna dauke da ita ba.”
Akwai likitoci 12 da suke kula da marasa lafiya a asibitin, shida daga cikinsu suna zagaya dakin da aka kwantar da marasa lafiya, yayin da kuma likitoci biyar ke duba marasa lafiyar da suke zuwa don ganin likita.
Dokta Auwal ya bayyana haka ne a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan rediyon Freedom da ke jihar Kano.
Yayin da yake amsa tambaya kan yanayin da kuma halin da asibitin yake ciki, Dokta Auwal yace: “Akalla kullum muna saida kati 150 daga Litinin zuwa Juma’a, wanda likitocinmu biyar ke duba wanda suka sayi katin”
Baya ga matsalar karancin likitoci, Dokta Auwal ya bayyana wasu matsalolin da suke fuskanta wanda suka shafi tsaftar asibitin, karancin gine-gine da kuma kayyyakin zamani don duba marasa lafiya da ke ziyartar asibitin.