Yayin da hadin gwiwa a fannin raya noma tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ke kara bunkasa, sassan masu sana’ar noma a kasashen Afirka na kara gano dabaru, da cin gajiya daga kwarewar kasar Sin a fannin raya wannan sana’a mai dimbin tarihi. A baya bayan nan wasu bayanai sun nuna yadda manoman kasar Kenya dake gabashin Afirka, ke murna da shigar sabbin magungunan kashe kwari masu inganci na kasar Sin cikin kasuwannin kasar, matakin da aka shaida kyakkyawan tasirin sa ga kiyaye yabanyar da manoman kasar ke samu yayin girbi.
Masana a fannin lura da amfanin gona na cewa, fasahohin kasar Sin na raya sana’ar noma, musamman bangaren yaki da kwari masu lalata amfanin gona, sun kai matsayi daidai da na kasashen da suka ci gaba, a wasu fannonin ma sun zarce hakan.
- Tsige McCarthy Daga Mukaminsa Ya Nuna Me Ake Nufi Da “Dimokradiyyar Amurka”
- Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo
A bangaren inganci da wadatarwa, da rashin hadari ma, magungunan kashe kwari na Sin da ke shiga kasuwannin Kenya, sun kai matsayin nagarta na kasa da kasa, wanda hakan ya sanya suke ba da gudummawa wajen inganta tattalin arzikin manoman kasar.
Don haka muna iya cewa, yayin da Sin ke samun karin tagomashi a fannin bunkasa fasahohin raya noma a cikin gida, da samar da karin yabanya mai yalwa a duk shekara, a hannu guda kuma, fasahohin ta na kara shiga sassan nahiyar Afirka, inda suke taimakawa manoma cin karin gajiya daga sana’ar su.
Ko shakka ba bu wannan shi ne fatan al’ummun Afirka, wato hadin gwiwa domin cimma moriya tare da kasashe masu ci gaba a dukkanin fannoni, wanda kuma tuni kasar Sin ta wuce sahun gaba a wannan muhimmiyar tafiya. Kuma daya daga muhimman gabobin tafiyar shi ne inganta noma a Afirka, da aiwatar da dukkanin matakai na zamani, na tabbatar da samar da isasshen abinci da al’ummar nahiyar ke bukata. (Saminu Alhassan)