• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwarewar Sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN)

by Bello Hamza
2 years ago
in Nazari, Manyan Labarai
0
Manyan Ayyukan Da Ke Gaban Sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Nada sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Dakta Michael Olayemi Cardoso, zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da daidaito a tsarin gudanar da babban bankin da irin ci gaban da ake bukata a halin yanzu don farfado da tattalin arzkin kasa.

Wannan kuma, kamar yadda masana da dama suke bayani tare da fashi bakin yadda nadin zai taimaka wajen warware manyan matsalolin da bangaren tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta musamman wadanda suke cutar da al’umma kasa.

  • Za Mu Tabbatar An Hukunta Masu Zaluntar Kananan Yara Da Mata – Kwamishina Rabi Salisu
  • Matsayin Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Japan Na Zuba Dagwalon Nukiliya A Cikin Teku Bai Sauya Ba

Wannan kuma yana zuwa n a daidai lokacin da shugaban kasa, a masatyinsa na kwararre ke yin abin da ya dace don tabbatar da tattalin arzikin kasa yana tafiya yadda ya kamata.

Kafin nada shi, Cardoso, wanda ma’aikacin banki ne kuma kwararren mai shirya harkokin al’umma, ya yi aiki a masatyin kwamishinan tattalihn arziki da tsare-tsaren kasafin kudi a karkashin Gwamna Tinubu a Jihar Legas. Duba da wannan ana iya cewa, kwararre ne a kuma yana da sanin makamin aiki na tafiyar da Babban Bankin Nijeriya, a matsayin wata cibiyar gwamnatin tarayya da ke da karfi a wajen gudanar da tsare-tasren kanana da matsakaitan masana’antu har ma da manyan masana’anatun kasar nan da abin da ya shafe su gaba daya. Wasu kuma na ganin wadannan kwarewa ba za su yi wani tasiri mai yawa ba in aka lura da cewa, wani tsohon shugaban Babban  Bankin Marigayi Alhaji Adamu Ciroma, ya karanta Tarihi ne a jami’a amma da marigayi shgugaban kasa Janar Murtala Mohammed ya nada shi ya yi aiki yadda ya kamata kuma ya ba mara da kunya, daga baya kuma aka nada shi a masatyin Ministan kudi saboda cancantarsa.

Amama dai koba komai yana ya hau karagar shugabancin ne a daidai lokacin da al’umma ke zura ido su ga irin tasirin da zai haifar musamman ganin yadda ake fuskantar mastalar hauhawar farashi, karyewar darajar Naira, da raguwar tasirin naira a kan kudaden kasashen duniya da kuma mastaloli da dama da suka yi wa tattalin arzikin kasa katutu.

Labarai Masu Nasaba

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

Adaidai wannan lokacin ne, mai sharhi zai tsaya ya yi Nazari don fahimtar cewa, Cardoso, wwanda ya yi karatun digiri a fannin gudanarwa a jami’ar Aston da ke Birtaniya ya kuma yi karatun babban digiri na biyu a jami’ar H Harbard ta kasar Amurka, tabbas wanann aiki ya yi daidai da shi.

‘Yan Nijeriya na masa fatan fara aiki nan take babu gudu babu ja da baya wajen samar da tsare-tsaren  da za su dawo da tattalin arzikin kasa hayyacinsa. Mutum zai samu kwarin gwiwa in aka lura da cewa yana a kan akidar shugaban kasa Asiwaju Tinubu kamar yadda ministan kudi Wale Edun, yake shima daga akidar Tinubun ya fito dukkan su za su taimaka wa juna wajen tabbatar da nasarar tattalin arzikin kasa, tare da samar da tsare-tsaren da za su taimaki shirin shugaban kasa na fitar da kasa daga kangin matsalolin tattalin arziki da suka yi wa Nijeriya katutu tun mulkin gwamnatiocin a suka shude.

Wannan al’amarin daukar mataki akan shi ya zama dole bama kamar yadda ake ma shi ganin shi na hannun daman Shugaban kasa Tinubu ne don haka wasu ke ganin yana  danyan ganye da shi.

Koda kuwa hakan gaskiya ne idan aka yi la’akari da irin siyasar Nijeriya wadda ta sha bamban da irin ta Legas, akwai abubuwan da sai an yi amfani da su musamman ma idan aka yi la’akari da yin  adalci kan al’amarin da ya shafi sashe ko bangaranci. akan ayyukansa a matsayinsa na gwamnan Babban Bankin kasa.

Wato dangane da yadda yake hulda da Shugaban kasa da kuma Ministan kudi, ya dai dace a tunatar da shi  ya dace ya daidaita yadda mizanin tafiyar tattalin arziki yakamata ya kasance, saboda al’amarin ya zama tamkar wata zumangiyar kan hanya ce da take bugun yaro da babba.

Wannan al’amari ko shakka babu ba karamin taimakawa yake ba wajen yadda tattalin arziki ya shafi rayuwa yake shafar rayuwar fiye  da tsammanin kowa, irin haka kuma ba za asaba da shi zai yi kuma a samincewa da al’amarin.

Ba sai ya tsaya an fada ma shi irin yadda al’umma suke matukar fuskantar wahala wajen tafiyar  da rayuwarsu ta yau da kullun, ba domin komai ba sai saboda yadda ake ta fuskantar matsaloli masu yawa wadanda ragon tattalin da ke fuskanta cutar  da ke da wuyar magani.

A matsayin sa na wanda yake da  wuka da nama na bangaren tattalin arziki sanin kowa ne shi ne mai ba Shugaban kasa shawara ta fannin tattalin arziki, kowa na san ran zai yi tunanin da zai taimaka wajen samar da hanya mafita ba ma sai ta fannin daya fi sani ba na tattalin arziki.Yana iya bullowa ta tsare- tsaren da za su taimakawa al’umma ba sai sun ji a jikinsu ba.Akwai ma al’amarin iya mu’amala da mutane hakan ma zai taimaka idan kuma ba ayi hakan ba, ba wani abin mamaki bane idan har an hadu da wani cikas ko matsala akan hanya.

Wani abinda ake ganin ya yi kaka-gida ko samarda katsalandan ba wani abu bane illa yadda aka dogara da shigo da kaya daga waje da kuma al’amarin siyasa yadda aka shigar da shi a abinda ya shafi kudaden kasashen waje nan ma dai  sa idon na  jada abubuwa su koma baya.

Idan har hakan ya zama gaskiyar  halin da ake ciki dole ne mukamin da aka bashi ya tsone idanun wasu, ba kuma wani abin mamaki bane aga wasu ko gane ba aji dadi ba kan mukamin da aka bashi saboda wasu bukatun da ake daga wurinsa ba dole ba ne a same su cikin kankanen lokaci ba.

Duk da haka dai ‘yan Nijeriya suan sa ran sai ya sa kafar wando daya da wasu har ma da wadanda  ake yi ma kallon sun fi karfin ayi masu hakan, muddin dai har ana son wajen lura da kudaden da sike asusun Nijeriya da yake waje, sanin kowa ne dai al’amarin yana tangal- tangal, sanin  kowa ne irin asusun ajiya dake waje shi ne yake taimakawa yawancin al’umma, kamar dai yadda idan aka yi ma al’amarin rikon sakainar kashi ‘yan kalilan ne za su yi facakar da zata sa al’umma cizon yatsa a haba.

Hakanan ma kafa ayi tsammanin wanda zai haua kujerar gwamann Babban Bankin kasa zai daga sau Banki ya ci gaba da zama mai tafiyar da harkokinsa, hakan kuma zai sa a kauce ma tunkarar akama wasu hanyoyin da za su sa ayi dana-sani akan wasu matakan da  ba za su iya taimakawa ci gaban tattalin arziki ba.

Lawal masanin tattalin arziki ne ya rubuto daga Legas


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Ta Jinjina Wa Kamfanin BUA Bisa Karya Farashin Buhun Siminti Zuwa Naira 3,500

Next Post

‘Yansanda A Delta Sun Kama Kananan Yara Da Laifin Fashi Da Makami

Related

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

6 hours ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

1 day ago
An San Masu ÆŠaukar Nauyin Boko Haram, Kariya Ake Ba Su – Tsohon Babban Soja
Manyan Labarai

An San Masu ÆŠaukar Nauyin Boko Haram, Kariya Ake Ba Su – Tsohon Babban Soja

1 day ago
Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Arewa: Ina Mafita?
Manyan Labarai

Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Arewa: Ina Mafita?

1 day ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Bukatar Farfado Da Cibiyoyin Bincike Don Bunkasa Kasa

2 days ago
EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
Manyan Labarai

EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo

2 days ago
Next Post
‘Yansanda A Delta Sun Kama Kananan Yara Da Laifin Fashi Da Makami

‘Yansanda A Delta Sun Kama Kananan Yara Da Laifin Fashi Da Makami

LABARAI MASU NASABA

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

August 23, 2025
Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

August 23, 2025
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

August 23, 2025
Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

August 23, 2025
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

August 23, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

August 23, 2025
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

August 23, 2025
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

August 23, 2025
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

August 23, 2025
Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.