Jakadan kasar Sin ya bukaci kasa da kasa da su taimakawa kasashen Afrika wajen warware matsaolinsu bisa bin hanyoyin da suka dace da yanayin kasashen.
Ya ce, “Muna kiran kasashen duniya da su goyi bayan kokarin da kasashen shiyyoyi ke yi wajen warware batutuwan dake shafar ’yan Afrika, a tsarin da ya dace da yanayin Afrikan,” Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana hakan a yayin taron kwamitin sulhun MDD kan batun jamhuriyar demokuradiyyar Kongo (DRC).
Mr. Dai ya ce, kasar Sin tana maraba da tattaunawar da ta gudana tsakanin gwamnatocin kasashen DRC da Rwanda, dangane da ci gaban da aka samu na baya bayan nan. “Kasar Sin tana goyon bayan kungiyar tarayyar Afrika, da sauran kungiyoyin shiyyar, wajen daga matsayin tattaunawa a tsakanin kasashen shiyyar, domin daidaita rikice-rikice.”
Jakada Dai ya kara da cewa, “Sin a shirye take ta cigaba da taka rawa wajen taimakawa kokarin da Kongo DRC ke yi, don cimma nasarar zama kasa mai ikon kanta, da kiyaye iko na yankunanta, da tabbatar da tsaron kasarta.” (Ahmad Fagam)