Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a ranar Lahadi cewa, a yanzu haka an kusa kammala aikin katafaren Kamfanin sarrafa karfe na Ajaokuta da aka yi watsi da shi a jihar Kogi, kamfanin zai samar wa ‘yan Nijeriya 500,000 guraben aiki da zarar an kammala aikinshi kuma an bude shi don kasuwanci ga kowa.
Shugaban ya kuma yi alkawarin mayar da karfi wajen ganin an kammala aikin Kamfanin domin zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar janyo masu zuba jari a kasar kai tsaye (FDI) da kuma samar da hanyar samar da ingantaccen yanayin kasuwanci da ake bukata domin kowane fanni ya samu ci gaba.
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Mutum 5,000 Sun Jikkata, Kusan 1,000 Sun Rasu.
- NDLEA Ta Cafke Wani Tsoho Mai Shekaru 67 Dauke Da Hodar Ibilis A Filin Jirgin Saman Abuja
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasa Tinubu, ya bayyana haka a wajen kaddamar da yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Lahadi.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi.
Da yake jawabi ga dimbin jama’a a Lokoja, Shettima, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya jajirce wajen ganin an kammala aikin kogin Neja da kuma aikin hanyar Kabba-Lokoja da Abuja-Lokoja.