A wani ba zata da ba’a taba tunaninsa ba, kasar Saudiyya ta dakatar da duk wata tattaunawar sulhu ko shiga tsakani tsakaninta da Isra’ila, kan sulhuntasu da kungiyar Hamas.
Saudiyya ta mika wa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, bayanan dakatar da shiga tsakanin, wanda kasar Amurka ke kan gaba wajen ganin sulhun ya yi wu, kamar yadda gidan talabijin na Samma’a TV ya rawaito.
- Sin Ta Nuna Bakin Ciki Kan Mutuwar Fararen Hula A Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Mutum 5,000 Sun Jikkata, Kusan 1,000 Sun Rasu.
Matakin na saudiyya, ya bar baya da kura kan makomar zaman lafiya da kuma yanayin dorewarsa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yanke alakar tattaunawar da kuma hukunci cire hannun kasar Saudiyan dai, ya jefa kasashe da dama cikin duhu kan ganin makomar kasashen biyu.