Bayan ‘yan kwanaki da kamfanin Simiti na BUA, ya sanar da rage farashin Simintinsa, amma bincike ya nuna cewa, farashin wasu kayan masarufi da kamfanin ke sarrafawa, musamman buhun Suga, buhun Fulawa katan din Taliya ya karu.
Mahukutan kamfanin dai, sun shelanta rage farashin buhun Simintin daya, a ranar 1 ga watan Oktoba zuwa Naira 3,500.
- Babu Maganar Dawo Da Tallafin Man Fetur – NNPCL
- An Horar Da ‘Ya’Yan Masu Bukata Ta Musanman Sana’o’in Hannu A Jihar Sokoto
Al’ummar Nijeriya sun yi farin ciki da samun ragowar farashin.
Sai dai, a bisa wani bincike da kamfanin labarai na nigeriantracker ya gudanar a wasu shaguna a fitacciyar kasuwar jihar Kano, ta gano cewa, an kara Naira N3,500 akan farashin buhun Suga, Naira N2, 000 akan buhun Fulawa da kuma Naira N1,000 akan katan din Talliya.
Bugu da kari, binciken jaridar ya nuna cewa, farashin buhun Suga a baya ana sayarwa akan Naira N44,000, katan din Taliya akan Naira N8,100, buhun Fulawa kuma akan Naira N32,500, amma a yanzu, farashin buhun Suga, ya kai Naira 47,500, buhun Fulawa akan Naira 34,500 sai kuma katan din Taliya daya akan Naira 9,000.
Wani dillali a Kano da ya nemi a saka ya sunansa, ya ce, karin farashin ya biyo bayan sanar da ragin da BUA ya yi ne akan Siminti.
A cewarsa, mun lura da karin farashin ne a makon nan da muke ciki. Kuma canjin farashin ya fito ne daga kamfanin kuma basu sanar damu ba kamar yadda suka saba.
Duk iya kokarin da aka yi don jin ta bakin mahukuntan kamfanin na BUA akan lamarin, ya cutura,