Djibouti tana arewa maso gabashin Afirka, kuma muhimmiyar kasa ce da ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, inda aka kafa cibiyar koyar da ilmin sana’o’i ta farko a nahiyar.
An nada wa cibiyar suna “Luban” daga sunan babban malamin samar da kayayyakin itatuwa a tarihin kasar Sin wato Lu Ban, domin koyar da fasahohin zamanin kasar Sin a Djibouti.
- Layin Dogo Tsakanin Sin Da Turai Ya Zama Babban Aiki Da Ma Alamar Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
- Gadar Sada Zumunta Tsakanin Sin Da Maldives
Yayin taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da aka shirya a watan Satumban shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kafa cibiyoyin koyar da ilmin sana’o’i na “Luban” guda goma a kasashen Afirka, domin samar wa matasan nahiyar damammakin koyon ilmin sana’o’in.
Kawo yanzu, jami’o’in kasar Sin sun riga sun kafa cibiyoyin Luban a kasashen nahiyoyin Asiya, da Afirka, da kuma Turai da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya sama da 20, inda matasan suke kokari domin cimma burinsu. Haka kuma, wannan dandalin hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren koyar da ilmin sana’o’i yana kara samun karbuwa daga al’ummun fadin duniya. (Mai fassara: Jamila)