Kwanan baya, kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “Shawarar ziri daya da hanya daya: Muhimmin jigo ga samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya”, inda aka yi cikakken bayani, da hakikanin alkaluma kan babban sakamakon da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata. Takardar ta nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yunin bana, kasar Sin da kasashe sama da 150, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 dake nahiyoyin biyar, sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 200 bisa shawarar.
Shawarar ziri daya da hanya daya, ta daidaita manyan matsalolin dake gaban yawancin kasashe masu tasowa a bangarorin cudanya, da raya tattalin arziki ta hanyar daukan hakikanin matakai, duk wadannan suna amfanar karin al’ummun kasa da kasa.
Takardar ta yi nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga ketare, kuma tana son kara zuba jari domin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, kana tana fatan karin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa za su shiga shawarar, ta yadda za a sa kaimi ga dauwamammen ci gaban dukkanin duniya. (Mai fassara: Jamila)