Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da Zamantakewa ta rayuwar yau da kullum, zaman Aure, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mutanen ke baje kolin hajar bayyana sirrikansu da zarar sun hau abun hawa, musamman mata. Sau tari a kan samu hakan daga wajen wasu matan yayin da suka shiga abun hawa sai su maida shi tamkar a tsakiyar falon gidajensu, wanda ya ke tafe a kasa ma yana jin hirar da suke yi, haka wanda ke cikin wata motar ma duk yana jinsu, ba sa tuna komai yayin da suke baje hajar ta su. Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Ko mene ne amfani ko rashin amfanin hakan?, wadanne irin matsaloli hakan ka iya haifarwa?, ta wacce hanya za a iya magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta. Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Tabbas mu mata muna da wannan halin, wanda akasarinmu hira ba ta dadi har sai an shiga Napep. Wanda kafin a kai inda ake son zuwa an baje kolin sirrukan da bai dace a watsar da su duka a cikin wannan dan tsukakken lokaci ba. Saboda ko daga masu hirar sai mai Napep suka yi aringizon fesar da abin da ke cikin bakunansu; to abin zai yi musu babbar illa, irin wacce ba za su taba zaton za su girbe abin da suka shuka a cikin wasu takaitattun dakikun da ba su wuce a kirga da yatsun hannu lba. Saboda ba kowace magana ce za ta yi wa mutum amfani a irin wannan lokacin ba. Amma wata idan an yi za iya ta ceto mutum daga halaka, yayin da wata idan an fasa rubabben ƙwai take zame wa mutum musiba da tonon asiri. Misali; akwai wata da ta dauko maita, suna tafe cikin Napep ita da kawarta. Suka fara tambayar juna kurwa nawa suka samo, daya ta ce ba su da yawa, daya ta ce ita kam ta samo da yawa. Don a cikin jakarta har da kurwar mahaifinta akwai. Har mai Napep ya ajiye su gidajensu, amma ya kasa natsuwa saboda tashin hankalin hirarsu da kunnensa ya debo masa. Jikinsa yana rawa ya koma gidansu wacce ta samo da yawa, ya yi sallama ya ce mai gidan yake nema. Aka ce da shi mai gidan bai da lafiya tsawon kwanaki ba zai iya fitowa ba. A take ya nemi ganin matar gidan, bai boye komai ba ya yi bayanin abin da kunnensa ya ji. Aka saka yarinya gaba ta bude jakar da ta saka kurwowin, sai ga fari suna ta fita a ciki suna tashi. Mintuna a tsakani mahaifinta ya mike daga zazzafan ciwon da ya kama shi. ‘Yan gidan da mutanen unguwa suka dinga jibgar yarinyar. Kafin dan lokaci unguwa ta karade da labari. Abun duba a nan, hira a Napep ta yi wa mahaifinta rana, kuma ita ta janyo mata falluwar sirri da jin kunya bayan kalolin tozarcin da za ta fuskanta a sanadin hakan. Babban hanyar magance wannan matsalar kame kai a ko’ina da kame baki muddin ba muhallin da ya dace ba. Shawara ga masu irin wannan halin; su daina, duk yadda zance ya matsi bakinsu su yi kokarin rufe abin su har sai sun fita Napep su furzar. Saboda wani daga lokacin da ya ji wani abu daga bakinka; to a duk lokacin da ya sake ganin ka ko ya ji labarin ka sai ya ce ai da bakinta ma na ji ta ce kaza. Allah ya ba mu ikon killace abin da ke zuciyarmu da bakinmu a wurin wadanda suka dace da inda ya dace mu fada.
Sunana Princess Fatima Mazadu:
Toh abu na farko dai abu ne na zubda mutuncin kai tsaye, dan ke abun hawa aka ce ba abun hira ba, sannan na biyu hatsari ne dan baka san da wa ka ke ba, abun hawan wa ka hau ba, nagari ne ko mugu ko maketaci?. Abun da zance anan kawai a kiyaye zamanin hira ya wuce yanzu koda akan gaskiya ne dan yanzu sai a nadeka bakinka ya jawo maka wahala. Ba shi da wata amfani sai zubda kima da gulma da rashin kamun kai. Sa kai hatsari ta kowacce hanya, ko alheri ne ba za ka bayyana a gaban wani da baka sani ba, bare wata kila tadin abun da ke faruwa a kasa ko gulmar wata ko wani Kowa ya hau abun hawa ya kiyaye harshensa, ya kama kansa ya san abun haya ya hau ba mallakinsa ba, sannan ya sa da bashi kadai ke tafiyar ba, sannan bai san kuma da su waye ake tafiyan ba. Ahhh! toh shawara kam kyeuta, in har ke mace ce mai tarbiyya sallama da bissmillah ya raba ki da abun hawa, surutu ba na mace mai daraja bane kwata-kwata. Mata mutuncin mu yafi komai a rayuwar mu, shi ya sa hallakamu ko tozarta mu ko keta mana haddi ba wahala a kiyaye sai Allah ya kara kiyaye wa, Allah ya sa mu dace.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya wannan ba kyakkyawar dabi’a ba ce ga mace, domin ita mace da kunya da yakana aka santa, don haka sakin baki a cikin abun hawa sam-sam ba dabi’a ba ce ta mace mai tarbiyya. To magana ta gaskiya hakan ba shi da wani amfani, hasali ma kamar wulakantar da kai ne musamman ga mace, domin duk wanda za ki gaya wa sirrinki babu wanda ki ke da tabbacin zai rike shi. Da farko dai su wadanda ki ke fadawar za rika yi miki kallon sha-sha-sha, mara kamin kai ko mara tarbiyya. Kuma hakan wulakantar da kai ne wanda ka’iya jawo wa wata rana idan ka kara haduwa da wadanan mutane suna maka kallon wulakanci. To akwai bukatar dai ‘yan mata ko mata su sani kunya, kamun kai, da yakana wasu abubuwa ne da ke karawa mace daraja, don haka duk macen data rasa su to rasa wani babban bangare na nagarta da maza suke so a wajen mace. To ni shawara ta ga duk mai irin wannan hali ya kamata ta canja, domin hakan ne kadai zai sa al’umma su ke ganinta da kima da kuma daraja, domin dukkanin macen da ta rasa kunya da yakana to ta rasa wani yanki na nagartar da maza suke so daga karshe nake addu’ar Allah ya shirye mu gaba daya.
Sunana Sani Mohammed Chindo, Unguwar Karofin Madaki Bauchi:
Tabbas akwai irin wadannan mutane da zarar sun shiga Napep ko motar haya za su rika zuba na surutu wanda hakan sam bai da ce ba. Ba shi da wani amfani yin hakan gaskiya, domin baka san da wa ka ke magana ba. Hakika akwai matsaloli mai tarin yawa da hakan ke aifarwa. Misali; Ka shiga motar haya da mutane da yawa baka san wa da wa ke cikin motar ba. Hanyar da za a maganace wannan dabi’a shi ne; duk lokacin da ka hadu da irin wadannan mutane ko suna surutun kai kayi gum da bakinka, idan ba ka amsa masa zai yi shuru. Sharawa ta ga masu irin wannan dabi’a su daina don babu kyau komai yana son sirri a rayuwa.
Sunana Hajara Ibrahim Jihar Bauchi:
A al’adar malam Bahaushe wannan sam! bai dace ba, wasu ma ko ba kowa da me Napep din suke zama su yi ta hira, wannan ba mutunci bane bai dace ba, kar ki kalli kanki matsayin budurwa, ko ke budurwa ce hakan ba mutunci, mazan ma su kansu sun fi son me kamun kai, sai kin fi burge kowa, ya kamata mu mata mu rinka kiyayewa muna kula da irin wadannan dabi’un.
Sunana Mika’ilu Na Bako GSWL LGA:
Gaskiya wanda suke hawa abun hawa musamman ma Mata su yi ta baje sirrinsu, hakikanin gaskiya hakan ba dai-dai bane, saboda bai kamata ace kina cikin abun hawa kuma kina zancen abun da yake faruwa a cikin gidanki ke da mijinki ba, saboda hakan na iya haifar da rabuwar aure, dan watakila matar da ki ke bawa labari za ta iya komawa daga baya ta je ta sake fadar abun da ki ka basu labari a wani gurin, daga nan har maganar ta koma wajan maigidanki, tom! idan bai kai zuciya nesa ba za ta iya kaiwa ga rabuwa. Ina bawa Mata shawara masu irin wannan hali da su daina hakan ba dacewa ba ce.
Sunana Auwal Muhammad, Kofar Mazugal Dala LGA:
Shawarata dangane da matan da suke zuba a cikin keke Napep
Ita ce ; Bai da amfani mace baki san da wa ki ke tare ba, baki san iya inda magnar da ki ka yi za ta tsaya ba, baki san irin kallon da na-tare da ke za su yi miki ba. Shawara mai yin hakan gaskia ta daina, don hausawa sun ce shiru ma magana ce.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA:
Maganar gaskiya ko maza yawan surutu barkatai bai dace a gare su ba balle mata, sabida ko addininmu ma baya son hakan, domin mafiya masu surutu za ka iya samunsu da karya da ma munafurci balle kuma ga mata, musamman matan aure sannan har ta kai suna fadar sirrinsu a cikin abin hawa na haya, wannan ba tsari bane, sannan ba koyarwar addinin Islama bane. Ba shi da wani amfani, sabida ai mu hausawa an san matanmu da kunya da kamun kai sai dai akwai wasu ballagazozin a cikinsu. Yin hakan yana haifar da matsala ta bayyana sirrin mazajensu da ma na iyayensu da kuma nasu sirrin. Idan ma ‘yan mata ne wasu suna ganin suna haka ne domin su burge mazan da suke kusa da su ko tare da su a abin hawan, to wallahi zubar da mutunci suke yi, domin duk namijin da yake kishin matarsa ba zai so ya auri ire-iren wadannan matan ba. Hanyoyin suna da yawa amma wadda nake ganin zai iya fada yanzu ita ce ke amatsayinki na ‘ya mace kina tuna cewa ke mace ce kuma an sanki da kunya sannan shi kansa sakin baki ako ina ba tarbiyya mai kyau bace domin na tabbata idan kina da aure kuma kuna tare da mai gidanki ba za ki iya hakan ba sannan idan ke budurwa ce ke ma ba za ki so ace saurayinki ya ganki kina aikata wannan dabi’ar ba. Su yi hakuri suna rike sirrinsu idan kuma ya zama dole sai sun yi surutun to su jira idan sun sauka su yi ko idan sun koma gida sai su fadi duk abin da za su fada din, domin a wannan surutun ne ake zakewa har a fadi sirrin wanda ma firarar ba ta shafe su ba, anan kuma kin ga kin ci naman mutum Allah ya sa mu dace.
Sunana Dayyabu Isa:
Gabaki daya hakan ba shi da wani amfani wani lokacin har da me abin hawan ake yin hira, idan hira takai hira sai ka ga matan sai ta gayyaci me abin hawan nan gidanta bayan bata sanshi ba bata taba ganinshi ba sai a lokacin.
Sunana Yahaya Umar Malumfashi Jihar Kano Hotoro:
Bai kamata mace ta zauna a Napep tana baje sirrinta dan a ka’ida mata ma kame bakinsu ya kamata su yi yayin da suke a hanya, dan muryarsu al’aura ce wannan ba daidai bane masu yi su ji tsoron Allah su daina.
Sunana Aleeyu Master:
Bai da amfani hakan, saboda baki san da wa ki ke tare ba, baki san iya inda mgnar da ki ka yi za ta tsaya ba, baki san irin kallon da na tare da ke za su yi miki ba. Shawara mai yin hakan gaskiya ta daina, don hausawa sun ce shiru ma magana ce.
Sunana Hafizu Yakubu:
Ni shawara ta anan shi ne; Ga masu yi hakan su daina ko dan kasancewarsu mata.
Sunana Ayshatu Bukar Sanda:
Gaskiya wannan ba mutumci ba ne ya kamata mata mu kula bare ma mace muryarta al’aura ce.
Sunana Madaki Isma’il Musa Jihar Kano Gezawa Dantsawa:
Shawarata shi ne; Ya zama dole mace ta ringa rike sirrinta ba dan komai ba sai dan ta boye sirrinta.
Sunana Isah Bujawa Jihar Kano Gedawa:
Rashin sanin mutuncin kai ne ya sa wasu matan suke bankade sirrinsu a waje ba tare da tunanin komai ba, amma dukkan mace me kamala, me mutunci me tarbiyya, me hankali, mai ilimi, to ba za ta yi haka ba.
Sunana Abdulkadir Ibrahim AKA Abdul, Jihar Kano:
Illa ce babba da rashin sanin darajar kai, mace ta saki baki tai) yi ta zuba a cikin Nafef/A daidata sahu, da mutanen da ba ta sani ba, a adddinance da al’adance bai dace ba, yana zubar da kima tare kawo illoli ciki har da mutanen banza, za su iya samun kofa da za su lalata rayuwar mace. Ya kamata mata su zama masu kamun kai, indai har mutun ba muharraminka ko makusancinka ba to bai kamata ka saki baki kayi ta surutu da shi ba, musammam a wannan yanayin da bata gari suka yi yawa.
Sunana Ibrahim Nguru:
Yin hakan na nuni da cewa idan abu marar kyau suke fada ko cutarwa watarana asirinsu zai tonu, saboda rashin sanin waye matukin keke Napep din.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya wannan dabi’un basu dace da mace mai kamun kai da sanin abin da ya kamata ba. Kuskure ne, ya kamata su gane su daina yi. Ba shi da wani amfani, rashin amfaninsa kuma shi ne bayyanin sirrinka ga wanda baka san kowaye shi ba, zai iya bibiyar sirrinka yayi maka illa, ta duk yadda baka za ta ba. Matsalolin da hakan zai iya haifarwa sun hada da barazanar tsaro kamar kidnapping, yi wa mutum sata ko kwace da sauransu. Sannan kuma da yiwuwar akwai wanda ya santa a cikin mutanen da suke cikin abin hawan ita bata sanshi ba, zai iya gaya wa mijinta duk abin da take cewa, shi ma ya ji. Hanyoyin magancewa sun hada da yawan fadakar da su, yi musu nasiha, jankunnensu a duk lokacin da za su fita daga gida, sai tsawatar masu a duk lokacin da za su yi hakan, koda ‘yan uwansu mata ne dake cikin abin hawan tare. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina don ba hali ne mai kyau ba, sannan rashin kunya ne da kamin kai, ya kamata su sani cewa sirri abu ne me muhimmanci a rayuwa.
Sunana Musbahu Muhammad, Gorom Dutse Jihar Kano:
Hakan bai kamata ba dan babu kamun kai a hakan. Ba shida amfani gaba daya dan ko me Napep din zai kalli me hakan a matsayin ballagaza. Yana bude hanyar barna a tsakanin mutanen da suke Napep din kuma yana zubar da kima da mutuncin masu yin hakan. Ta hanyar nasiha da jan hankalin nasu irin hakan a media da sauransu. Ya kamata su sani cewa mace duk inda take an santa da kamun kai, Nutsuwa da kuma iya baki.