A yau Talata ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da takwaransa na kasar Najeriya Kashim Shattima a nan Beijing, wanda ke halartar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa dangane da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya karo na 3.
A yayin ganawar, Han Zheng ya ce, kasar Sin na yin hangen nesa kan daidaita hulda tsakaninta da Najeriya bisa manyan tsare-tsare. Tana kuma fatan kara amincewar juna a tsakaninta da Najeriya ta fuskar siyasa, da hada kai wajen zamanantar da kasa, a kokarin samar da abun misali na hadin gwiwar manyan kasashe masu tasowa.
Ya ce a cikin shekaru 10 bayan da Sin ta gabatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, shawarar ta kasance hajar da kowa zai ci gajiyar ta a duniya, kuma dandalin hadin gwiwa da kasashen duniya suka amince da shi. Ya kara da cewa, Najeriya, kasa ce da ta fara shiga hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wajen raya shawarar. Kana kasar Sin na son zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da Najeriya a sassa daban daban, a kokarin ba da jagora wajen daga matsayin hadin kan Sin da Afirka.
A nasa bangare kuma, Kashim Shattima ya ce, Najeriya na gode wa kasar Sin bisa goyon bayan da ta dade tana ba ta, da ma kasashen Afirka baki daya. Ya ce shawarar ta Ziri Daya Da Hanya Daya ta ba da jagora mai muhimmanci, kan hadin kan kasashen duniya ta fuskar samun ci gaba. Kuma Najeriya na son inganta hadin gwiwar moriyar juna da Sin, da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare. (Tasallah Yuan)