Majalisar Wakilai ta jaddada aniyar mayar da hankali wajen amincewa da kasafin kudi na shekarar 2024 kafin karshen watan Disambar wannan shekarar.
Majalisar wadda ta bayyana hakan a yau Talata ta ce, za ta amince da kasafin ne don a samu wanzar da kasafin a tsakanin Janairu zuwa Disamba.
- Najeriya Ta Yi Imanin Shawarar BRI Za Ta Inganta Ci Gaban Kasashen Afirka
- Mahara Sun Hallaka ‘Yan Sintiri 9 A Bauchi
Shugaban kwamtain tantance kudi na Mjalaisar, Abubakar Kabir Bichi ne ya bayyana hakan.
Ya ce, majalisar za ta yi aiki da ka’idojin da tuni aka tabbatar da su domin a kiyaye dokar hada-hadar kudi don amnincewa da kasafin kudin kafin ranar 21 na watan Disamba.
Kazalika, Bichi ya ce babu wata tantama da za a wanzar da kasafin kudi a tsakanin Janairu zuwa Disamba.
Ya ci gaba da cewa, doka ta 20 da ka’ida ta 15 na majalisar ta shekarar 2020 ne suka bai wa kwamatin tantace kudi na majalisar karfin iko sa ido da duba yadda ake kashe kudi tare da amincewa da kasafin kudi bayan majalisar kasa ta amince.
Bugu da kari, ya bayar da tabbacin cewa, kwamitin, zai gana da shugaban kwamtin kula da harkokin kudi, da na tsare-tsare da na karbo rance da mahukuntan sashen kula da bashi don kawamtin na sa ya yi aiki yadda ya kamata don a wanzar da kasafin kudin ta hanyar sanya ido yadda ya dace.
Bichi kazalika ya sanar da cewa, kwamtin zai kuma tabbatar da ya yi hadaka, musamman da sauran kwamitoci na majalisar dattawa da sauran masu ruwa da tsaki domin a tabattar da yin gaskiya wajen amincewa da kasafin kudin.