Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano karkashin jagorancin S.A. Amobeda, ta yanke hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 ga wani dillalin tabar wiwi, Muhammad Bako Sambo.
Sambo na daga cikin masu safarar miyagun kwayoyi guda bakwai da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta gurfanar da su a watan Oktoba.
- Najeriya Ta Yi Imanin Shawarar BRI Za Ta Inganta Ci Gaban Kasashen Afirka
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Agazawa Bunkasuwar Afirka
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya raba ga ‘yan jarida a Kano jiya, inda ya nuna cewa an samu Sambo da laifi kuma an yanke masa hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali.
Sadiq, ya ce an samu nasarar daure mai laifin ne bisa kokarin kwamandan hukumar, Abubakar Idris Ahmad.
Sadiq, ya kara da cewa NDLEA ta tashi tsaye wajen yin aiki tukuru domin dakile dukkanin ayyukan safara da shan miyagun kwayoyi, ya kara da cewa, samun nasarar daure dilar kwayoyin wata alamar nasara ce da ke nuni da cewa masu yunkurin safarar tabar wiwi su sani Kano ba wurin cin burinsu ba ne.
“Sambo, wanda ya kasance mai safarar tabar wiwi daga Ondo da wasu jihohin kudancin Nijeriya zuwa wasu jihohin arewacin Nijeriya, ya fada hannu ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020.
“Jami’an NDLEA da ke aikin sintiri a kan hanyar Kano zuwa Zariya ne suka kama shi a lokacin da suka ga wata mota kirar Honda da suke zarginta, an cafke wanda ake zargin ne a Hotoro da ke Kano.
“Da aka kaddamar da bincike an gano cewa Sambo ya dauko wiwi mai nauyin kilogiram 201 a motarsa. Kuma asalinsa mazaunin Lokogoma da ke Abuja.”
Sanarwar ta kara da cewa kotun ta daure Sambo ne bayan gwajin da aka yi kan tabar wiwin.
Ya kara da cewa, kwamandan hukumar Ahmad ya jinjina wa kokarin tawagar jami’ansu bisa kokarinsu wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi da nasarar da suka samu a kotun.