• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kada Ku Bari ‘Yan Bindiga Su Shafe Mu Baki Daya – Baraje

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Baraje

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bosso/Paikoro a jihar Neja, Hon. Yusuf Kure Baraje, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen ceto al’ummar mazabarsa daga ayyukan ‘yan fashin daji. 

Dan majalisar ya ce halin rashin tsaro da al’ummar mazabarsa ke fuskanta abu ne da ke neman daukar matakin gaggawa domin matsalolin tsaro na kara ta’azzara.

  • Majalisar Wakilai Za Ta Amince Da Kasafin Kudin 2024 Kafin Karshen Disamba
  • Najeriya Ta Yi Imanin Shawarar BRI Za Ta Inganta Ci Gaban Kasashen Afirka

Ya ce, “Misali, a kauyena an kai hare-hare kusan sama da 10, ‘yan fashin har farfajiyata suka shigo suka farmake ni. A yanzu da nake magana da ku, ban taba ganin wani soja da aka tura domin yakar ‘yan fashin dajin a maboyarsu ba.

“Lokaci daya da sojoji suka zo zagayen bincike daga sansaninsu na Kantiri a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna amma babu sojojin da aka jibge a Neja da ke zaune takanas don dakile aniyar ‘yan bindiga.”

Ya nuna takaicinsa kan yadda masu garkuwar ke cin karensu babu babbaka duk kuwa da cewa suna kara jefa jama’a cikin matsin tashin hankali a kowane lokaci.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

Ƙazalika ya ce, babu wani yunkuri da sojoji ke yi na ganin bayan ‘yan fashin dajin a halin yanzu.

Ya roki gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yiyuwa domin cimma ‘yan fashin dajin a maboyarsu domin kawo karshen su cikin gaggawa don kauce wa yunkurin ‘yan fashin na share al’ummar kauyukan jihar daga muhallansu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Majalisar Dattawa
Labarai

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Labarai

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Next Post
Za Mu Dasa Wa ‘Yan Nijeriya Dabi’ar Gaskata Kalaman Shugabanni A Zukatansu – Minista

Za Mu Dasa Wa 'Yan Nijeriya Dabi'ar Gaskata Kalaman Shugabanni A Zukatansu - Minista

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.