Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD ya jaddada cewa, dole ne a mayar da batun tsagaita bude wuta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila daga dukkan fannoni ba tare da bata lokaci ba a gaban komai.
Zhang ya yi wannan furuci ne a gun taron gaggawa da kwamitin sulhu na MDD ya yi jiya 18 ga wata don tattauna halin da Palasdinu da Isra’ila ke ciki, inda ya bayyana cewa, babu wanda zai yi nasara a cikin yaki, dole ne a yi watsi da matakan soja, a dawo kan taburin tattaunawa. Kana, dole a bar kai wa fararen hula hari, a kuma martaba dokar jin kai ta duniya. Bugu da kari, Sin na kan ra’ayin cewa, hanya mafi dacewa ta warware rikicin Palasdinu da Isra’ila ita ce a koma kan “shirin kafa kasashe biyu”.
A ranar, daftarin kuduri da Brazil ta gabatar kan batun Palasdinu da Isra’ila ya samu amincewa daga mambobin kwamitin sulhu guda 12, amma saboda kuri’ar Amurka ta kin amincewa ce, daga karshe dai ba a zartas da kudurin ba. Zhang ya bayyana matukar kaduwa da bacin ransa game da batun. (Kande Gao)