Yayin wata zantawa da manema labarai a baya bayan nan, shugaban wani kamfanin sarrafa magunguna dake kasar Faransa, ya ce yayin da baje kolin kayayyakin shige da fice na kasa da kasa na kasar Sin ko CIIE karo na 6 ke karatowa, kamfanoni da dama masu jarin waje, na shirin baje nasarorin su a fannin kirkire-kirkire. Irin wadannan kamfanoni na fatan gina kyakkyawar makoma tare da kasar Sin, a gabar da manufofi, da tarin damammaki da tattalin arzikin Sin ke samarwa ke kara bunkasa karfin gwiwar kamfanoni, tare da zurfafa cimma nasarori tare da Sin.
Wasu alkaluma da gwamnatin Sin ta fitar a jiya Laraba, sun nuna gamsuwar da kamfanonin Sin masu jarin waje ke nunawa, sakamakon bayanan ci gaban tattalin arzikin Sin a rubu’i 3 na farkon shekarar bana.
- Sin Ta Yi Kira Da A Tsagaita Bude Wuta A Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila Ba Tare Da Wani Jinkiri Ba
- Peng Liyuan Da Sauran Matan Shugabanni Mahalarta Taron BRF Sun Ziyarci Gidan Adana Kayan Fasaha Na Sin
Alkaluman dai sun nuna GDPn Sin cikin wannan wa’adi ya karu da kaso 5.2 bisa dari a shekara, adadin da ya haura na wasu kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
A tsawon lokaci, wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya na yawan yayata batun “Janyewar jarin waje daga kasar Sin”, da nufin nuna gazawar tattalin arzikin Sin. To sai dai kuma, shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa, kamfanoni masu jarin waje dake Sin na ta karuwa, kuma da dama daga cikin su na samun kyakkyawar riba.
A farkon watan Nuwamba, sama da kamfanoni 3400, daga kasashe da yankunan duniya 128, za su hallarci bikin baje kolin CIIE karo na 6.
Karuwar ‘yan kasuwa dake tururuwar shiga kasuwannin Sin na shaida cewa, jita-jitar da kafofin yammacin duniya ke yadawa game da gazawar tattalin arzikin Sin, ba ta da wani tushe ko makama. (Mai fassara: Saminu Alhassan)