Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta da ke sintiri a kan titin Buruku-Birnin Gwari a yayin da suke sintiri na yau da kullum a Udawa kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a ranar Litinin din da ta gabata, sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da suka futo don Garkuwa Da matafiya.
Lamarin wanda ya afku a kusa da kauyen Masallaci da ke kan hanyar, an yi artabu tsakanin jami’an da ‘yan bindigar da ke dauke da muggan makamai.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Muhammed JaIge, ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a garin Kaduna, ta ce jami’an ‘yan sandan tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun nuna jarumtaka da ba a saba gani ba wajen tunkarar ‘yan Bindigar wanda hakan ya bada nasarar dakile kwanton baunar, Kuma dole ‘yan bindigar suka ja da baya.

‘Yan Bindigar sun tsere cikin dazuka bayan samun raunukan harbin bindiga Daban-daban, sun bar bindigar AK47 guda daya da kuma babura guda hudu.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar yankin da su sanya ido ga duk wani mutum da aka gani da raunin harsashi sannan su kai rahoto zuwa ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa domin daukar matakin gaggawa.