Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana yayin ganawa da manema labarai na yau da kullum jiya Alhamis cewa, kasar Sin ta yi matukar takaicin yadda Amurka ta ki amincewa da kudurin kwamitin sulhu na MDD, wanda ya kai ga a dakatar da ayyukan jin kai a Gaza.
A ranar Laraba ne dai, kudurin da Brazil ta gabatar, ya samu goyon bayan kasashen kwamitin 12 daga cikin 15. Amurka, wacce ke da ikon hawa kujerar naki, ita ce mamba daya tilo da ta kada kuri’ar kin amincewa da kudurin, yayin da kasashen Birtaniya da Rasha suka kauracewa kada kuri’a.
- Rikicin Gaza: Ana Ci Gaba Da Tir Da Kisan Fararen Hula A Harin Asibiti
- Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina
Mao ta bukaci kwamitin sulhun da ya saurari kiran da kasashen Larabawa da al’ummar Palasdinu suka yi, da taka rawar da ta dace wajen ganin an tsagaita bude wuta, da kare fararen hula da kuma hana fadadar bala’in jin kai.
Sannan, jakadan kasar Sin na musamman kan harkokin Gabas ta Tsakiya ya jaddada shirin kasar Sin na taka muhimmiyar rawar da ta kamata wajen saukaka tankiyar dake tsakanin Falasdinu da Isra’ila, tare da ingiza tattaunawar zaman lafiya.
Zhai Jun ya bayyana haka ne yayin ziyararsa a yankin Gabas ta tsakiya.
Jakadan ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na bakin ciki da yanayin matsalar jin kai da aka shiga a yankin, haka kuma tana Allah wadai da dukkan ayyukan dake haifar da illa ga fararen hula tare da adawa da keta dokokin kasa da kasa.
Ya kuma bayyana cewa ainihin dalilin da ya haifar da yanayin da ake ciki shi ne, gazawa wajen kare halaltattun hakkokin Falasdinawa. (Ibrahim Yaya, Fa’iza Mustapha)