Bana ake cika shekaru 110, da kafuwar kungiyar daliban kasar Sin dake kasashen Turai da Amurka, wato kungiyar sada zumunta tsakanin daliban kasar Sin dake karatu a kasashen ketare, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya aika sakon taya murnar sa, domin isar da gaisuwa da fatan alheri gare su.
A cikin sakon na sa, Xi ya yi nuni da cewa, kungiyar daliban kasar Sin dake kasashen Turai da Amurka, kungiyar jama’a masu zurfin ilmi ce dake karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma tun kafuwarta, a ko da yaushe tana taka rawar gani, wajen hada kan daliban dake karatu a ketare, domin bautawa kasar Sin inda aka haife su, da jama’ar kasar.
Xi ya jaddada cewa, a sabon zamanin da ake ciki, ya dace kungiyar ta kara ba da gudumowarta a bangarorin kishin kasa, da gabatar da shawarwarin masana, da gudanar da harkokin waje tsakanin jama’a, da cudanyar wayewar kai tsakanin Sin da ketare, ta yadda za ta taimaka ga ingiza raya kasa, da farfadowar al’ummar kasar ta Sin. (Mai fassara: Jamila)