A yau Litinin ne aka bude babban taron wakilan mata na kasar Sin karo na 13 a nan birnin Beijing.
Shugabannin Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) da na kasa, ciki har da Xi Jinping, da Li Qiang, da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi da Li Xi, sun halarci bikin domin taya su murna.
- Kasar Sin Ta Bukaci Tsagaita Wuta Da Samar Da Agajin Jin Kai A Zirin Gaza
- Kashim Shettima: Kasar Sin Ta Kasance Mai Kaunar Zaman Lafiya Da Bunkasar Arzikin Duniya
Ding Xuexiang, ya gabatar da jawabi a madadin kwamitin kolin JKS, inda ya taya murnar bude taron, tare da mika gaisuwar ban girma ga mata da masu aikin ci gaban mata a fadin kasar, da kuma ‘yan uwa mata na yankunan musamman na Hong kong da Macao, da kuma Taiwan, da matan Sinawa mazauna kasashen waje.
A cikin jawabinsa, Ding ya bayyana irin gagarumar gudunmawar da matan kasar Sin suka bayar tun bayan babban taron wakilan mata na kasar karo na 12. Ding ya yi kira ga mata a fadin kasar da su sauke nauyin da ke wuyansu a wannan sabuwar tafiya.
Kimanin wakilai 1,800 ne suka halarci taron, tare da wakilai 90 da aka gayyata na musamman daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao, sun halarci taron. (Yahaya)