• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mun Damu Kan Bayyanar Mayakan Kungiyar Ansaru A Yankinmu — Mutanen Birnin Gwari

by Abubakar Abba
2 years ago
Ansaru

Mazauna  Kauyen Kuyello a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, sun nuna damuwarsu kan bayyanar ‘yan ta’addar Ansaru a yankunansu. 

An ruwaito cewa, ziyarar bazata a ‘yan kwanan baya da ‘yan Ansarun suka kai akan baburansu a yankunan, hakan ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankunan na karamar hukumar.

  • Matashin Dan Kwallon Barcelona Guiu Mai Shekaru 17 Ya Jefa Kwallon Farko A Kungiyar
  • Asalin Kungiyoyin Mayakan Hamas, Hizbullah Da Manufofinsu

Kazalika, an ruwaito cewa, wasu daga cikin mazauna yankunan sun gargadi ‘yan kungiyar ta Ansaru da su fice daga yankunan su.

Bugu da kari, rahotannin sun ce, “‘yan Ansaru na gudanar da ayyukansu a kauyukan Kazage, Unguwar Gwandu, Unguwar Gajere, da kuma tsohon garin Kuyello, inda suke jan ra’ayin matasa suna shiga cikin kungiyar ta Ansaru domin su kara yawan adadin ‘ya’yan kungiyar a karamar hukumar. ”

Wani babba daga cikin mazauna kauyen, Malam Muhammadu Kuyello, ya tabbatar da cewa, ‘yan Ansaru sun shiga cikin Kuyallo ta hanyar garin Dan Auta, inda suka wuce, ba tare da sun ce wa kowa uffan ba.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

Kazlika, ya sanar da cewa a yanzu haka, Ansaru sun dauki kimanin matasa 50 na tsohon garin Kuyallo a cikin kungiyarsu, inda kuma suka aurar da ‘yan mata bakwai.

A cewarsa, idan gwamantin jihar ta tura jami’an tsaro zuwa tsohon garin Kuyello, ‘yan kungiyar ba su da wani zabi illa su arce daga garin.

Bugu da kari, wani jagoran matasa a yankin  Baban yara Isa, ya ce, idan har mahukunta ba su kawo dauki ba, mazauna yankin za su yi artabu da ‘yan kungiyar da nufin fatattaksrsu daga yankin.

Ya ce, tuni masu fada aji a yankin suka sanar da mahukunta daban-daban da ke karamar hukumar akan lamarin, inda ya yi kira ga mahukuntan da su gaggauta daukar mataki.

Shi ma shugaban ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) Ishaq Kasai, ya tabbatar da lamarin.

Sai dai, kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Kaduna ASP Mansir Hassan ya ce, bai da hurumin yin magana akan lamarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Xi Ya Jaddada Jan Hankalin Ma’aikata Da Su Shiga Aikin Farfado Da Kasa

Xi Ya Jaddada Jan Hankalin Ma’aikata Da Su Shiga Aikin Farfado Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.