Game da kalamai masu alaka da kasar Sin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi a baya-bayan nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau a kullum Larabar nan cewa, wadannan kalamai tamkar yin watsi ne da gaskiya, kuma cike suke da kuskure, da tunani da akidar yakin cacar baka, da son zuciya.
Don haka kasar Sin tana adawa da su matuka.
Rahotanni sun bayyana cewa, sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana a wani taron kungiyar tsaro ta NATO a kwanan nan cewa, kasar Sin na kokarin dakile tsarin kasa da kasa da yake da tushe.
Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, jawabin na Blinken cewa NATO “ba ta neman rikici” munafunci ne karara, kuma bai dace da gaskiyar lamari ba. Tarihin NATO na daya shi ne, tayar da rikice-rikice da yake-yake.
Kama daga Bosnia da Herzegovina zuwa Kosovo, da Iraki, Afganistan, da Libya, da Ukraine, a zahiri kungiyar tsaro ta NATO da ke da’awar cewa, ita ce kungiyar kare kai, ita ce take keta yankuna da iyakoki, tana tayar da yaki tana kashe fararen hula da ba su san hawa ba balle sauka, kuma har yanzu babu abin da ya sauya.
Zhao Lijian ya ce, har kullum, kasar Amurka ta kan fifita dokokin cikin gida a kan dokokin kasa da kasa, kuma ta yi amfani da dokokin kasa da kasa, a lokacin da ya dace, kuma ta yi watsi da su idan ba su dace da moriyarta ba. Wannan shi ne babban cikas ga tsarin kasa da kasa.(Ibrahim)