Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke ziyara a kasar Amurka, ya tattauna da masana tsara manufofi na Amurka da ’yan kasuwa na kasar a jiya Asabar a birnin Washington.
A lokacin da yake tattaunawa da masana tsara manufofi na Amurka, Wang Yi ya ce, yayin ziyararsa, bisa yanayi na daidaito da girmmama juna, Amurka da Sin sun yi tattaunawa mai zurfi kuma mai ma’ana kan batutuwan dake jan hankalinsu, haka kuma sun aike da kyakyyawan sako game da daidaitawa da inganta dangantakarsu.
- Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wang Yi
- Wang Yi: Akwai Bukatar Mayar Da Dangantakar Sin Da Amurka Bisa Tafarki Mai Aminci Da Dorewa
Ya kara da cewa, duk da sabani da takkadamar dake akwai tsakanin kasashen biyu, da tarin batutuwan da ba a shawo kansu ba, bangarorin biyu sun yi imanin cewa, ya zama wajibi kuma abu ne mai amfani su ci gaba da tattaunawa a matsayinsu na manyan kasashe.
A nasu bangare, mahalarta tattaunawar sun bayyana cewa, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka ta dace da muradun kasashen biyu. Haka kuma, za ta taka muhimmiyar rawa wajen warware muhimman batutuwan yankuna da na duniya baki daya.
Sun kara da cewa, yayin da ake fuskantar rikice-rikice a yankuna da rashin oda a duniya, ya zama wajibi Amurka da Sin su karfafa tuntubar juna da hada hannu wajen shawo kan kalubale.
Sannan a lokacin da da yake tattaunawa da wakilan kungiyar ’yan kasuwa ta Amurka Wang Yi ya yi fatan kungiyar ’yan kasuwa ta kasar Amurka, za ta kyautata ra’ayin jama’a da karfafa tubalin abotar Sin da Amurka, da kuma bayar da sabbin gudunmuwa ga ingantawa da raya dangantakar kasashen biyu. Ya jaddada cewa, har yanzu dangantakar kasashen biyu na da karfi.
Mahalarta tattaunawar sun ce, muradun Sin da Amurka na hade da juna, kuma dangantaka mai karfi a tsakaninsu, na da muhimmanci ga nasararsu baki daya. Haka kuma, kungiyar tana bayar da muhimmanci ga ci gaban Sin mai inganci, kana tana da kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Sin da goyon bayan kasashen biyu wajen daukar matakan da suka dace na saukaka musaya tsakanin jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)