An gudanar da taro game da harkokin kudi na kwamitin kolin JKS a birnin Beijing, daga jiya Litinin zuwa yau Talata, inda sakatare janar na kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ya gabatar da jawabi.
Xi Jinping, shugaban kasar Sin kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya nazarci kalubalen da samar da ci gaba mai inganci a bangaren harkokin kudi ke fuskanta tare da tsara ayyuka masu ruwa da tsaki da za a yi yanzu da kuma nan gaba. (Fa’iza Mustapha)