Majalisar wakilai ta rushe bukatar siyan jirgin ruwan shugaban kasa da aka tanada acikin kasafin kudi, ta mayar da kudin da aka ware zuwa tsarin rancen dalibai na gwamnatin tarayya, wanda hakan ya kara yawan kudin daga naira biliyan 5.5 zuwa naira biliyan 10 a cikin karin kasafin kudin shekarar 2023.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan amincewa da karin kasafin kudin.
- Majalisa Ta Amince Da Karin Tiriliyan 2.17 A Kasafin Kudi Na 2023
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
“Abinda muka sani a kasarmu, shugaban kasa ba shi da jirgin ruwa, don haka, mun mayar da kasafin zuwa shirin lamunin dalibai na gwamnatin tarayya.
“Idan za a iya tunawa, lamunin daliban ya kai Naira biliyan 5 a cikin kasafin kudin, amma mun kara shi zuwa Naira biliyan 10,” inji shi.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, gwamnatin tarayya ta gabatar da kudirin ware naira biliyan 5.095 domin siyan jirgin ruwan shugaban kasa a cikin shirin karin kasafin kudin shekarar 2023.