A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da bikin nuna al’adu na kasar Sin da Najeriya.
Dalibai daga makarantun gwamnati 12 dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun yi dafifi a cibiyar al’adun kasar Sin, wurin da ake gudanar da bikin al’adun Sin da Najeriya na shekarar 2023, domin fafatawa a tsakaninsu a fannoni biyu, wato raye-rayen kasar Sin da raye-rayen Najeriya.
- Kyawawan Manufofin Tattalin Arzikin Sin Na Kara Karfafawa Kamfanonin Ketare Gwiwar Shiga Babbar Kasuwar Kasar
- An Kaddamar Da Yankin Gwaji Na Cinikayya Maras Shinge A Xinjiang
Ofishin jakadancin kasar Sin dake a Najeriya da hukumar kula da ilimin sakandare na babban birnin tarayyar Najeriya FCT suka shirya bikin.
An inganta mu’amalar al’adu a tsakanin kasashen biyu, kuma ya zuwa yanzu bikin al’adun Sin da Najeriya ya zama “sanannen sha’anin al’adu”, a cewar Li Xuda, mai ba da shawara kan harkokin al’adu na ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya.
Sin da Najeriya jiga-jigai ne masu dogon tarihi wajen riko da al’adu. Al’ada na taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin tarihin ‘yancin kai da farfadowar kasarmu, cewar Li. (Mai fassara: Yahaya)