Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda ta kaddamar da bada tallafin Naira dubu 50 ga mata dubu hudu don dogara da kai wajen harkar sana’arsu.
Hajiya Huriya Dauda ta kaddamar da tallafin ne yau a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
- Ina Da Kwarewar Shugabancin Majalisa Fiye Da Akpabio – Ndume
A wajabinta, Huriya Dauda ta bayyana cewa, kamar yadda kuka sani, wannan gwamnati babban Kudirin ta shi ne taimakon rayuwar mutane, musamman marasa galihu, akwai bukatar karfafawa da tallafa wa mata, kuma mata sama da dubu hudu a fadin jihar za su ci gajiyar wannan tallafin na Naira dubu 50, in ji Huriya Dauda”.
“Mun yi haka ne don ganin iyayenmu mata su zama masu dogaro da kansu, tare da lura da kalubalen da ake fuskanta sakamakon tabarbarewar tattalin arziki”.
“Wannan shirin karfafawa na sana’a ya yi nisa ne domin tallafa wa mata dubu hudu a fadin jihar da naira dubu 50 domin rage radadin wahala da kuncin rayuwa da ake ciki.
Ina rokon ku da ku yi amfani da kudin wajen yin kananan kasuwancin da kuka zaba ko kuma wace kuke yi a yanzu a gidajenku.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Fatima Ibrahim ta bayyana godiyarta ga Allah da kuma addu’a ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal na cimma kudirinsa na ci gaban jihar Zamfara baki daya.